Jarumi Ali Nuhu ya karɓi ragamar aiki a matsayin Shugaban NFC

  • Ya sha alwashin bunƙasa harkokin finafinai

Daga BASHIR ISAH

Jarumi a masana’antar Kannywood, Dokta Ali Nuhu, ya kama aiki a hukumance a matsayin Shugaban Hukumar Fina-finai ta Ƙasa (NFC).

Sanarwa mai ɗauke da sa hannun Daraktan Hulɗa da Jama’a na hukumar, Brian Etuk, ta nuna a ranar Talata Ali Nuhu ya shiga ofis a matsayin shugaban hukumar na bakwai.

Ta ƙara da cewa, jarumin ya sha alwashin yin aiki tukuru don bunƙasa masana’antar fina-finai ta Nijeriya.

Da yake jawabi a wajen bikin karɓar ragamar aiki wanda aka shirya a hedikwatar hukumar da ke Jos, babban birnin Jihar Filato, Ali Nuhu ya ce zai yi amfani da ƙwarewarsa wajen ciyar da masana’antar fim ta Nijeriya gaba.

Ya yi amfani da wannan dama wajen gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, (GCFR) bisa naɗin da ya yi masa.

Kazalika, ya yi alƙwarin mara wa tsare-tsaren Ministar Ƙere-ƙere da Al’adu Barr. Hannatu Musawa baya na neman bunƙasa fannin shirya finafinai.

Mahalarta taron sun haɗa da Sakataren Tace Finafinai na Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha; Ƙungiyar MOPPAN; Barr. Ezra Jinang SSA ga Gwamnan Filato; Alhaji Sani Muazu; Sir. Eward Fom; Alfred Mgbejume, Achor Yusuf da sauransu.