‘Yan binga sun sace mutum 61 a wani sabon hari a Kaduna

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga jihar Kaduna sun ce aƙalla mutum 61 wasu da ake zargin ‘yan fashin daji ne suka yi garkuwa da su a yankin Buda da ke cikin Ƙaramar Hukumar Kajuru a jihar.

Duk da dai babu bayani a hukumance ka aukuwar harin, sai dai wani mazaunin yankin ya shaida wa majiyarmu ranar Talata cewar, maharan sun dira ƙauyen ne da misalin ƙarfe 11:45 na dare inda suka yi awon gaba da mutum 61.

A cewar Dauda Kajuru wanda mazaunin yankin ne, ‘yan bindigar shiga yankin da yawansu, kuma sun harba bindiga.

Ta bakinsa, “abin da ya faru jiya tashin hankali matuƙa. Maharan sun shigo ne da nufin kwashe mutane sama da ɗaliban firamaren da aka yi garkuwa da su a ƙauyen Kuriga na Ƙaramar Hukumar.

“Sai dai ankarewar da sojoji suka yi a kan kari ya sa adadin waɗanda aka yi awon gaba da su ya taƙaita.

“Ƙannena na daga cikin waɗanda aka yi garkuwa d su jiya, kuma bayanan da muka samu da safe shi ne, har yanzu maharan ba su isa sansaninsu ba tukuna.”

Ya koka kan cewa tun bayan da aka ɗauke Kwamandan sojoji da aka fi sani da Tega a yankin, harkokin ‘yan bindida suka dawo a ƙauyukan yankin Ƙaramar Hukumar Kajuru.

Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da ‘yan bindiga suna sace ɗaliban firamare sama da 200 a yankin Kuriga, lamarin da gwamantin jihar ta ce ta sha alwashin za ta ƙwato yaran ba tare da wani ya ji ko da ƙwarzane ba.