Yanzu-yanzu: Majalisar Dattawa ta dakatar da Ningi na wata uku kan zargin cushen kasafi

Majailisar Dattawa ƙarƙashin jagorancin Sanata Godswill Akpabio, ta dakatar da Sanata Abdul Ningi na tsawon wata uku daga majalisar.

Manlisar ta ɗauki wannan mataki ne yayin zaman da ta yi ranar Talata, kuma ta dakatar da Ningi ne bayan da ya yi zargin an yi cushe na Naira tiriliyan 3.7 cikin Kasafin 2024.

A wata hira da BBC Hausa ta yi da ɗan majalisar mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya kwanan nan, aka ji shi ya ce haƙiƙanin kasadin 2024 da aka gabatar Tiriliyan 25 amma ba Tiriliyan 28 da ake amfani da shi a halin yanzu ba.

Ya ce bayan wakilta ƙwararru da suka yi don nazarin kasafin na bana, sun gano an yi cushe na Tiriliyan N3.

Da farko mamba a Kwamitin rabon kasafi na majalisar, Sanata Jimoh Ibrahim, shi ne ya miƙa ƙudurin a dakatar da Ningi na tsawon watanni 12 kan zargin da ya yi.

Daga bisani an samu wasu sanatoci da suka mara wa ƙudurin Jimih Ibrahim baya, sai sun buƙaci a rage wa’adin dakatarwar zuwa wata shida da wata uku.

A ƙarshe, sanatocin sun amince da a fakatar da Ningi na tsawon wata uku bayan da Shugaban Majalisar ya bada damar kaɗa ƙuri’ar jin ra’ayi.

Sanata Ningi ɗan babbar jam’iyyar hamayya ne, wato PDP, kuma Shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewa.