Ana fargabar yara biyu sun mutu sakamakon gobara a sansanin ‘yan gudun hijira a Borno

Bayanan da MANHAJA ta kalato daga Jihar Borno a wannan Talatar sun ce, an samu aukuwar gobara a Sansanin ‘Yan Gudun Hijira da ke yankin Muna a Maiduguri a jihar.

Duk da dai babu wani bayani a hukumance, amma wasu majiyoyi sun ce gobarar ta yi ajalin wasu yara guda biyu.

Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, ba a kai ga gano dalilin da ya haifar da gobarar ba.

Haka nan, ‘yan sanda a jihar ko gwamnati, babu wanda ya ce uffan kan lamarin kawo yanzu.

Jihar Borno na daga cikin yankun da suke fama da hare-haren Boko Haram sama da shekara 10 lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, kana ya ɗaiɗaita dubbai.