An ga watan Ramadan a Saudiyya

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Kotun Ƙolin Saudiyya ta ce gobe Litinin shi ne zai zama 1 ga watan Ramadan na 1445 biyo bayan ganin jinjirin watan da aka yi da yammacin Lahadi.

Da wannan ake sa ran al’ummar musulmin ƙasar su tashi da azumi a ƙasa kamar yadda jaridar Arab News ta rawaito.

By Editor