Tinubu ya hana likitoci tafiya hutu ƙetare

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta sanya dokar hana fita hutu ga likitoci da ma’aikatan jinya da sauran ma’aikatan kiwon lafiya da sukan ƙetare zuwa yin hutu a waje.

Ƙaramin Ministan Lafiya, Dokta Tunji Alausa, shi ne ya bayyana haka ranar Asabar a Abeokuta.

Ya ce daga yanzu, dole ma’aikatan lafiya da ke zuwa ƙetare neman aiki su yi nurabus kafin su tafi.

Ya ƙara da cewa, wannan umarni na ƙunshe ne cikin umarnin da Shugaban Ƙasa Tinubu ya bayar.

A cewarsa, an ɗauki wannan mataki ne domin magance ƙalubalen da ake fuskanta a ɓangaren kula da lafiyar ƙwaƙwalwa.

Kazalika, Ministan ya ce gwamnati ta fara gudanar da shirin ɗaukar sabbin ma’aikata a fannin kiwon lafiya don magance matsalar ƙarancin ma’aikata a ɓangaren.