Ku mayar wa ‘yan kasuwa kayan abinci da kuka ƙwace, umarnin Tinubu ga Hukumar Kwastom

Daga UMAR GARBA a Katsina

Babban Kwantorola na Hukumar Hana Fasa-ƙwauri ta Ƙasa, Bashir Adewale Adeniyi, ya ce Shugaban Ƙasa asa Bola Ahmed Tinubu, ya ba wa hukumar umarni a kan ta mayar da kayan abinci da ta ƙwace daga hannun wasu ‘yan kasuwa don sake kai su kasuwanni a sayar wa ‘yan ƙasa.

Shugaban hukumar ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki a garin Kwangwalam dake iyakar ƙaramar hukumar Mai’adua a jihar Katsina.

A cewarsa, umarnin mayar da kayan abincin, wani jinƙai ne daga Shugaba Tinubu da kuma tabbatar da cewa al’umar ƙasar nan sun sami isasshen abincin da za su saya cikin farashi mai rahusa a kasuwanni.

“Manufar mayar da kayan shine don a samar da abinci tare da tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya ba su zauna da yunwa ba, don haka Shugaban Ƙasa na duba wannan a matsayin ɗaya daga cikin tsare-tsare da za su taimaka a tunkari matsalar ƙarancin abinci.” Inji shi.

Sai dai ya ce za a mayar da kayan abincin da aka ƙwace bisa sharaɗin masu kayan za su kai su kasuwanni don sayarwa a kasuwannin dake faɗin ƙasar nan.

“Mun ƙwace manyan motoci guda 120 da aka loda masu kayan abinci za a kai ƙasashen waje, wanda hakan yana nufin an kwashe abinci mai tarin yawa daga kasuwanninmu wanda ya haddasa ƙarancinsa, hakan kuma yasa farashin abincin ya hauhawa. Saboda haka muna fata lokacin da za mu mayar da waɗannan kayan abinci a kasuwanni hakan zai rage tsadarsu. ” Inji shi.

Shugaban hukumar ya kuma ziyarci tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a gidan shi dake Daura daga nan ya zarce zuwa gidan Mai Martaba Sarkin Daura Umar Faruq Umar don sada zumunci.