Gobara ta tashi a tashar lantarki a Kano

Daga BASGIR ISAH

Tashar wutar lantarkin da ke Dan’Agundi a Jihar Kano ta kama da wuta a ranar Lahadi.

A cewar wani jami’in Kamfanin Lantarki (TCN) a Kano, gobarar ta shafi wasu manyan tiransifoma da ke tashar.

Ya ce, “Ni ma ba na ofis, yanzun nan ake sanar da ni wutar ta shafi tiransifoma biyu, amma guda daga ciki na aiki.

“Haka nan akwai wani guda da ba a fara aiki da shi ba, shi ma wutar ba ta shafe shi ba.”

Da yake amsa tambaya, jami’in ya ce abin da ya faru ba zai hana tashar ci gaba da aiki ba.

Ya ce duk da dai an ɗauke wutar a halin yanzu, za a maido da wutar bayan an ƙura ta lafa.

Har zuwa lokacin da aka kammala haɗa wannan rahoto, ƙoƙarin jin ta bakin Kakakin Hukumar Kwana-kwana na Kano, Saminu Yusif Abudullahi, ya ci tura.