20
Sep
Daga AISHA ASAS Rundunar ‘yan sandan Afirka ta Kudu ta kaddamar da bincike kan mutuwar mata bakwai da aka gano gawarwakinsu a yankin Ekurhuleni, gabashin birnin Johannesburg, cikin watanni biyu da suka gabata, lamarin da ya sake jefa jama’a cikin fargaba kan tsaron mata a kasar. Rahotanni sun ce wasu daga cikin matan an same su ba tare da tufafi ba ko kuma da kadan daga cikin tufafinsu, yayin da wasu gawarwakin ke dauke da alamomin cin zarafin mata. Mafi yawancin wadanda abin ya shafi mata ne ‘yan shekaru 20 zuwa 30, yayin da daya daga cikinsu ta kasance matar…
