23
Aug
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce babu wata tattaunawa da ke gudana tsakanin Amurka da Iran, yayin da Tehran ta ce har yanzu mashigar ruwan Hormuz a rufe take, lamarin da ya sake jefa shirin kawo ƙarshen rikicin ƙasashen biyu cikin rashin tabbas. Trump ya bayyana hakan ne ranar Talata, 18 ga Agusta, 2026, inda ya ce babu wata tattaunawa da aka shirya yi tsakanin Washington da Tehran. Ya kuma dage cewa mashigar Hormuz a buɗe take, kuma ana iya zirga-zirgar jiragen ruwa a cikinta. Sai dai Iran ta musanta hakan, inda ta ce ba za ta buɗe mashigar ba…
