Hajjin 2024: Nijeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna

Daga BASHIR ISAH

An cimma yarjejeniyar aikin Hajjin bana tsakanin Gwamnatin Nijeriya da takwararta ta kasar Saudiyya.

A ranar Lahadin da ta gabata bangarorin biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a Jedda, kasar Saudiyya, inda Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya wakilci Gwamnatin Nijeriya.

Yayin wani taron ban gishiri, in ba ka manda da suka yi tare da Ministan Hajji da Umarah na Saudiyya, Dokta Taofiq bin Fawzan AlRabiah, Tuggar ya bayyana cewa ayyukan Hajjin 2024 za su gudana ne bisa sabbin dokokin da aka gindaya domin tabbatar da komai ya gudana a kan lokaci.

Tattaunawar tasu ta tabo muhimman batutuwa da suka hada da batun jigilar maniyyatan Nijeriya da kamfanonin jiragen saman da gwamanati za ta sahale wa yin aikin jigilar da dai sauransu.

 “Mun tattauna yadda za a inganta ayyukan Hajji da Umarah, wannan abu ne wanda ake nazarinsa a kowane lokaci. Kuma daga abin da muka tattauna, za a ga cigaba game da ayyukan Hajji a wannan shekakarar,” in ji Tuggar.

A nasa bangaren, AlRabiah ya ce hukumomin Saudiyya za su duba dukkan matsalolin da Minista Tuggar ya gabatar tare da ba da tabbacin samun cikakken hadin kan hukumomin kasar na bangaren Hajji da Umarah don cimma nasara a Hajjin bana.

Shugaban Hukumar Aikin Hajji na asa  (NAHCON), Malam Jalal Ahmad Arabi da sauransu da Mukaddashin Ambasadan Nijeriya a Saudiyya, Mahmud Lele na daga cikin wadanda suka shaida rattaba hannu a yarjejeniyar.