Shin kashe Al-Arouri ya kashe Hamas?

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Duk wani yaki na bukatar manyan dakaru da kan zama ginshikai kuma a ke daukar wa imma umurni daga wajen su ko koyi da irin jarumtakarsu. Mun dai san cewa tun watan Oktobar bara a ke gwabzawa tsakanin Isra’ila da kungiyar HAMAS ta Falasdinawa da ke jagorantar yankin Gaza.

Yakin dai tamkar tsakanin mai jifa da dutse ne da mai zarerren takobi ko ma fiye da haka na makaman gayawa jini na wuce. Sojojin Isra’ila na amfani da jiragen yaki, tankunan yaki da manyan bindigogi kan ’yan HAMAS. Su kuma ’yan HAMAS na cilla rokoki ko amfani da duk abun da ya sauwaka wajen tunkarar sojojin na Isra’ila.

Wannan tsari na HAMAS ya sa wasu ke ganin kasada ce babba ko sayar da rai ne HAMAS ke yi. Ba ma kawai jiragen yaki Isra’ila ke amfani da su a yakin ba, in ta kama jiragen ruwan yaki ma za su shigo cikin fafatwar da Firaminista Benjamin Netanyahi ke muradin na murkushe HAMAS ne gabadaya. Wato abun dubawa yadda yakin ya dau ke gab da shiga watan a hudu tsakanin kasa da a ke ganin ta na da rundunar da babu irin ta a tagomashi a duniya wato Isra’ila da Zirin Gaza da ke cikin yankunan duniya da mutane ke zaune cikin takaicin rayuwa da rashin ‘yanci.

Gaba daya ma masu rike makamai a cikin ‘yan HAMAS nawa ne? shi kan sa Zirin na Gaza na da mutum miliyan 2.3 wato gaba dayan sa kenan da mata da maza da kowa da kowa. Yayin da Isra’ila ka iya samun taimakon makamai ko ma ta na da damar sayo karin makamai daga turai, ‘yan HAMAS sai dai su yi amfani da dabarun su ko fasahar su wajen kera ‘yan abubuwan da su kan yi amfani da su musamman in an duba yadda su ka faro yakin nan daga kai hari yankin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktobar bara.

Yadda suka ratsa shingen lantarki da kamarorin tsaro har suka kai harin babban abun mamaki ne. Ba mamaki hakan ya sa masu ganin sam ba haka ba ne ke cewa da gangan Isra’ila ta bari a kai yakin don samun damar ragargaza yankin Gaza.

Ga bayanai daban-daban da ke fitowa. Mu dai a nan mu na amfani da abun da ya fito a zahiri ne na tarihin fitinar da kuma yanda a ka kirkiro kasar Isra’ila daga kasar Falasdinawa a 1948.

Abinda ya kan kawo mai karamin karfin makami ya rika arangama da mai babban makami shi ne zuciyar kwatar ’yanci da kuma maida mutuwa wata aba ce ta gwarzantaka da sadaukar da kai ga sauran masu zuwa na baya don su ci moriyar ’yanci.

Hakika da mutuwa na hana mutane motsawa ko bayyana kukan su, to tun shekaru gommai Falasdinawa sun daina komai sai zama tamkar masu hidima ne ga Yahudawa. Cikin Falasdinawa akwai musulmi masu rinjaye da kuma mabiya addinin Kirista. Jakadan Falasdinawa a Nijeriya Abdallah Shawesh ya ce akwai Yahudawa da ke marawa Falasdinawan baya. Shawesh ma bai amince da ambatar yakin tsakanin Yahudawa da Falasdinawa ba ne amma sai dai a ce arangama tsakanin gwamnatin Isra’ila mai mamaya da kuma Falasdinawa da a ka dannewa hakki.

Isra’ila ta kashe daya daga manyan jigogin HAMAS a harin jirgi marar matuki a yankin Dahiyeh da ke kudancin kasar Lebanon.

Saleh Al-Arouri na daga cikin kimanin mutum 6 da harin ya hallaka a wani bene da jirgin ya jefawa boma-bomai.

Dama Amurka ta ayyana ba da ladan dala milIyan 5 ga duk wanda ya samar da labarin inda za a samu Al-Arouri.

Kashe jigon ya kawo tunanin yiwuwar kara rincabewar fada a yankin Gaza yayin da a ke sa ran samun sassaucin zubar da jini da a ke yi.

Gidan talabijin na HAMAS a manhajar TELEGRAM ya bayyana cewa wasu daga wadanda su ka rasa ran su akwai shugabannin sashen soja na HAMAS mai taken Al-Qassam da su ka haxa da Samir Findi Abu Amer, da Azzam Al-Aqraa Abu Ammar. Wadannan manyan jigogi ne a tafiyar HAMAS da gwagwarmayar da ta ke yi.

Motocin daukar marar sa lafiya sun taru a gaban benen don daukar wadanda su ka samu raunuka zuwa asibiti inda a ka ga hannaye da naman mutane a gefen titi.

Firaministan Lebanon Najib Mikati ya yi Allah wadai da harin inda ya ce Isra’ila na neman shigar da Lebanon cikin yakin na Gaza.

Kashe waxannan manyan dakaru bai nuna alama ta kusa ko nesa cewa HAMAS za ta yi saranda ko ta kunce damarar cigaba da fafatawa ba.

Isra’ila ta shiga aikin janye dubban sojoji daga arewaci zuwa kudancin Gaza don maida hankali kan wasu ssasa na yankin.

Kakakin sojan Isra’ila Daniel Hagari bai bayyana ko hakan ya nuna Isra’ila za ta sauya dabara ko shiga wani babin yaqin ba ne, amma ya ce Isra’ila na shirye don dogon yakin da ta ke yi.

Yakin ya raba dubban Falasdinawa a Gaza da matsugunan su cikin mutum miliyan 2.3 an kai ga kashi 80% sun bar gidajen su.

Kazalika fiye da Falasdinawa 21, 800 su ka rasa ran su akasarin su mata da kananan yara.

Isra’ila na daukar matakin ne daidai lokacin da sakataren wajen Amurka Anthony Blinken zai kawo ziyara yankin kuma Amurka ke bukatar Isra’ila ta sassauta yakin da ta ke yi.

Abun damuwar a nan shi ne Falasdinawa daga Gaza sun kaura zuwa yankunan da Isra’ila ta kebe a kudanci kamar garin Khan Younis amma hakan bai hana Isra’ila jefa boma-bomai ba a yankin.

Matakin na Isra’ila ya sa Falasdinawa daukar ba ma wani yanki da ya zama tudun mun tsira. Hatta garin Rafah da ke kan iyakar Gaza da Masar ma inda Falsdinawan ke komawa ya kan zama kowane lokaci da yiwuwar fadowar bom kan mutane farar hula.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce yakin da sojojin sa su ke yi kan Gaza na kare kai ne kuma su na kokarin yin sassauci iya iyawa wajen zubar da jinin da su ke yi.

Netanyahu na magana ne a ganawa da majalisar sa a birnin Tel’Aviv.

Firaministan na martani ne kan matakin da Afirka ta kudu ta dauka na shigar da karar kasar Yahudawan gaban kotun duniya a birnin Hague don a tuhume ta da kisan kare dangi kan Falasdinawa.

A nan Netanyahu ya ce ba wai kisan kare dangi Isra’ila ke yi ba amma HAMAS su ke yaka da ya yi ikirarin in an bar HAMAS za ta kashe su gabadaya. Ba a dai fahimci ko Netanyahu na nufin yaqin murqushe dukkan ‘yan HAMAS da hakan ko nuna kashe su gaba daya ba kisan kare dangi ba ne don su dangin da a ka sallamar ne.

Yayin da sojojin Isra’ila ke cigaba da ruwan wuta a kan Zirin Gaza inda dubban Falasdinawa su ka rasa ran su, Masar na bayyana shirin da zai kai ga dakatar da yakin.

A nan Masar ta ce ta na jiran amincewa ko amsar sassan biyu na Isra’ila da Hamas kafin yanke matsayar.

Tsarin na Masar ya hada da sakin kamammu a hannun Hamas da kuma sako Falasdinawa da Isra’ila ta dankare gidajen yarin ta da su.

Kazalika Masar ta ce za a kuma kawo sabon tsarin yanda za a gudanar da mulkin Gaza bayan daina yakin.

Yayin da Isra’ila ke amfani da dukkan karfin niyyar gamawa da duk wani dan Hamas da hakan kan kare kan mata da kananan yara; Falasdinawa na nuna ba saranda kan gwagwarmayar kwato ‘yancin kasar su.

Wani limami da a ka budewa wuta a kusa da masallaci a Newark da ke New Jersey a Amurka ya riga mu gidan gaskiya.

Limamin mai suna Hassan Sharif na aikin tsaro ne a sashen sufuri kuma an tabbatar limami ne.

Jami’an ‘yan sanda sun garzayo bayan samun labarin harbin Sharif inda tuni a ka kaddamar da bincike don gano musabbabin kisan.

Bayanai sun nuna yaqin da Isra’ila ta ke yi da HAMAS a Gaza ya kawo zaman zullumi na kin jinin Musulunci a sassan Amurka.

Kammalawa;

Ko wata nawa wannan sabon yakin da Falasdinawa su ka lakaba wa NAKBA 2 wato kisan kiyashi na biyu zai kai, lokaci ne zai nuna. Siyasar duniya ta sa Larabawa kan yi kaffa-kaffa da yadda su ke maida martani kan yakin na Gaza.

Katar da Masar kan yi zagi ne wajen sararawar yaqi na kwanaki ta hanyar sharadin sakin kamammu da fusrsunoni. Kawai Falasdinawa na yaqi ne ba tare da tunanin samun tallafin da zai iya wuce imanin su na kwato kasar su daga mamayar Yahudawa. Rashin fargaba kan iya ba wa mutum nasara a lamura da dama don ba mamaki wanda ya fidda tsoro daga zuciyar sa ya iya firgita wanda ke tankar yaki da ke jin tsoron rasa ran sa. Ai an ga wata mata Bafalasdiniya rike da jaririn ta da a ka kashe ta na gode wa Allah maimakon kukan ta mutu ta lalace.

Wannan darasi ne da ke nuna duk abun da mutum ya sa a gaba da iya gaskiya da imanin sa, to ture shi na da wuyar gaske kuma ko ya kau zai samu wanda zai dora daga inda ya tsaya.