Abin da ’yan Nijeriya ke buƙata a 2024

Shekarar da ta gabata, 2023, shekara ce da ta zo da kalubale ga ‘yan Nijeriya. Ta zo ne da zazzabin gabatowar babban zaben 2023 tare da zuwa karshe da munanan hare-haren ta’addanci a Jihar Filato a lokacin Kirsimeti.

Dangane da wahalhalun tattalin arziki da ya biyo bayan matakin farko na tattalin arziki na sabuwar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, gwamnatin ta yi bayanin cewa hakan ne farkon kuma karshen zafin rayuwa ga ‘yan kasa a cikin sabon tsarin fatan shugaba Tinubu.

Sai dai kuma a wannan shekara ta 2024 akwai wasu abubuwa da ’yan Nijeriya ke son ganin sun faru a kasarsu domin tabbatar musu da cewa fatansu na ganin Nijeriya ta gyaru bai fadi kasa banza ba.

Da farko dai shi ne sake fasalin zabe da kuma matsayin bangaren shari’a a cikin tsarin siyasa. Tabarbarewar babban zaben 2023 da kuma shari’o’in kotun sauraron kararrakin zabe.

Gwagwarmayar da ’yan Nijeriya da dama da kungiyoyin farar hula suka yi na samun dokar tabbatar da na’urar tantancewa da watsa sakamakon zabe daga rumfunan zabe da kuma dora makamancin haka zuwa babban dakin kallo domin kauce wa magudin sakamako a cibiyoyin tattara sakamakon zaben ya ci tura. Haka dokar da aka baiwa hukumar gudanar da zabe, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta nuna akasin haka.

Yadda INEC ke gudanar da zabukan gaba daya ya sa mutane da yawa suka yi kira da a karfafa dokar zabe domin ta zama tilas ta amince da masu kada kuri’a da kuma yada sakamakon ta hanyar lantarki a zabe mai zuwa.

Har ila yau, a karon farko a Nijeriya, zaben 2023 ya samar da shugaban kasa da kuri’u marasa rinjaye. Shugaba Bola Tinubu ya samu kusan kashi uku kacal na yawan auri’un da aka kada a zaben shugaban kasa.

Ya kamata a yi la’akari da dokar zabe don samar da wanda ya yi nasara a kowane mukami na zartarwa – shugaban kasa, gwamna ko shugabannin kananan hukumomi – da akalla kashi 50 na kuri’un da aka kada ko a zaben farko ko zagaye na biyu.

Har ila yau, batutuwan da suka taso a shari’ar karar zabe sun bukaci da a kara yin sauye-sauye ga dokar zabe. ’Yan Nijeriya dai na son a warware duk wasu kararrakin da ke gabanin zaben kafin zabe mai zuwa, sannan a yi watsi da duk wasu kararrakin zabe a kotu kafin rantsar da wadanda suka yi nasara.

Haka kuma ’yan Nijeriya na son a samar da hukumar INEC mai cin gashin kanta ta hanyar nada jami’anta domin fitar da masu ra’ayin bangaranci.

Abin da ke da alaka da wannan shi ne kada wasu alkalai kalilan su yanke hukunci kan wanda ya yi nasara a zabe.

Idan alkalai sun ga laifin zabe, sai ’yan takara su koma rumbun kada kuri’a domin samun hakkin jama’a. Duk wadannan suna bukatar karin gyara ga dokar zabe.

Rashin tsaro na rayuwa da dukiyoyi na tayar da hankalin ‘yan Nijeriya. A wannan kasar, yawancin masu aikata laifuka suna tafiya a kan tituna ba tare da izini ba.

Sun hada da kananan barayi da masu damfarar kudi zuwa ‘yan fashi da makami da masu kisa da masu garkuwa da mutane da ’yan ta’adda. ’Yan Nijeriya dai na bukatar hukumomin tsaro da za su iya ganowa tare da hana aikata laifuka da hukunta masu laifi.

Ana son aikin ’yan sanda da na soja su rika samun bayanan sirri da amfani da fasahar sa ido, ba wai wanda ake amfani da shi a halin yanzu ba, in ba haka ba labarin mai alfarma Sarkin Musulmi, Saad Abubakar III – na cewa ‘yan fashi da masu laifi a ko da yaushe sun kere wa hukumomin tsaro – zai cigaba da kasance.

Abin da ke faruwa a yanzu – inda ’yan bindiga suka kai wani gagarumin farmaki a kan al’ummomi kusan 20 a Jihar Filato na tsawon kwanaki biyu ba tare da dakile su daga hannun jami’an tsaro ba. Dole ne shugabanni su bijire wa irin wannan rashin imani idan gwamnati na son a dauki mataki da gaske.

A fannin tattalin arziki, ’yan Nijeriya na son a rage musu wahalhalun da suke yi a baya. Halin hauhawar farashin kayayyaki a kashi 27.33 bisa 100, wanda hauhawar farashin kayan abinci ke a kashi 32.8 (ya zuwa ranar 15 ga Disamba), yana jefa dimbin ‘yan kasa cikin kunci, fiye da kashi 63 cikin dari na ’yan Nijeriya matalauta ne masu dumbin yawa (‘yan kasa miliyan 133) kamar yadda kasar ta ayyana ta Ofishin Kididdiga a cikin 2021.

’Yan Nijeriya dai na son gwamnati ta samar da mafita cikin gaggawa don shawo kan matsalar wuatar lantarki da karancin abinci da ke jefa al’umma cikin mawuyacin hali.

A dunkule, ’yan Nijeriya na son jami’an gwamnati su yi koyi da dabi’ar gaskiya da adalci: su gaina gaya wa ‘yan Nijeriya masu fama da matsalolin tattalin arzikin da su qara sadaukarwa a lokacin da su kansu ke rayuwa ta almubazzaranci da kuma yin almubazzaranci da dukiyar jama’a.

’Yan Nijeriya kuma suna son majalisar dokoki ta kasa su kasance masu gudanar da aikinsu na sa ido a bangaren zartarwa da na bangaren shari’a na gwamnati, ba wai kame hannun syu waje guda ba.

’Yan Nijeriya ba sa son gwamnati ta qara yin lamuni da rashin amfani da kudaden da aka ranta.

Tuni dai Nijeriya ke amfani da sama da kashi 95 cikin 100 na kudaden shigarta na kasa wajen biyan basussukan da ake bin su ba. Maimakon haka, ya kamata gwamnati ta samar da hanyoyin samun kudaden shiga na cikin gida a cikin ma’aikatunta, sassanta da hukumominta, galibi ta hanyar balaguro zuwa aasashen waje.

A karshe dai ’yan Nijeriya na son a kara raba madafun iko ga kananan hukumomi bisa tsarin Gwamnatin Tarayya.

A matsayinmu na jarida muna yi wa ’yan Nijeriya fatan alheri a shekarar 2024.