Sana’a da arziki a ma’aunin hankali suna da alaƙa ta ƙud da ƙud – Kamal

Daga AMINA YUSUF ALI

Kamal Alkasim wani masani ne a fannin kasuwanci da tattalin arziki wanda ya gogu a harkar. Ga wasu shawarwari da ya bai wa masu sana’a don inganta rayuwarsu ta fannin tattalin arziki:

A wannan lokacin da yawan masu sana’a kama ya yi su kara wa sana’o’insu kishiyoyi , wannan kuma ba shi da ita ya rungume ta domin ita ce silar samun arziki tilo. Duk arziki yana kunshe cikin sana’a domin ita ce hanya ingantacciya ta samunsa.

Rungumar sana’o’i kanana da matsakaita ga matasanmu wannan zai zama kamar juyin juya halin yaqar talauci a wannan lokaci da muke ciki dake cike da kuncin rayuwa.

Babu shakka duk sana’a za a iya kallonta a matsayin hanyar neman arziki komai girman kuma komai kankantarta a tattare da mai yin ta.

A lokacin da matasa ke cike da zalamar son yin arziki dare daya , to dole su sa a ransu , sana’a Ita ce silar duk wani arziki da suke gani. Ta hanyar sana’a ne kawai mutum zai iya tunkarar birnin da ake samun arziki a rayuwa domin ita ce guguwar da za ta tallafe shi domin isa wannan gurin.

Sana’a da arziki aminan juna ne domin: duk lokacin da daya bai ga daya ba dole wani ya nemi wani domin daya ba zai rayu ba tare da danuwansa ba.

Har na tuna da maganar Shugaba Abubakar Tafawa Balewa a cikin littafinsa na Shaihu Umar ya ce “In da ake da yalwar arziki akwai karancin tsegumi a wannan guri”, tabbas maganarsa haka ne , arziki na yalwata ne ta sanadin sana’o’in dake samowa suna kara tallafa masa haka shi zai zamar masa taki na habbaka da kuma girbar tarin alkhairai a cikinsa.

Akwai wasu dalilai da nake ganin za su iya hana sana’a ta yi wa mai ita abin da yake bukata , saboda illarsu ga sana’a , wannan dalilan su ne:

Raina sana’a: Raina sana’ar da ka ke yi hakan zai ba ka damar kin daukarta da mahimmancin ita kuma sana’a ‘yar halak ce , sai ka mutuntata sannan za ta mutunta ka.

La’antar Sana’a: La’antar sana’ar sana’a na zamar silar lalacewarta , la’antarta na nufin ita ba ta da muhimmanci , wanda kuma hakan rashin basira ne.

Hangen Sana’a: Masu hangen sana’ar wasu a matsayin ita ce mai albarka ba ta su ba, su ma suna zalamar waccen sai su bar tasu ta watse, wannan dalilin na sa su iya kassara sana’arsu ba tare da sun samu waccan ba.

Shafci-fadin masu sana’a: Da yawa masu sana’a idan suna bayar da labari ga wasu yadda sana’arsu ke samar musu da dimbin riba, wasu shafci-fadi da karairayi ne kawai domin burge wanda suke ba wa labari. To idan aka hadu da mai karancin nazari hakan na sa shi fara neman Wacce ba tare da auna bayanin da aka yi masa ba.

Sana’ar ya yi: Wasu matasan na yin sana’ar da ake ya yin ta, da kuma ta wuce za su kara chanja ta saboda su ya yi suke bi wanda hakan ya yi dai-dai da ra’ayoyinsu.

Canje-canjen sana’a: Canje-canjen sana’a na hana mutum ganin tasirin sana’a a rayuwarsa , duba da bai tsaya ya fahimci dukkaninsu ba don haka ba zai son wuyarsu da ribar dake cikinsu ba.

don haka nake gani dagewa da jurewa da rashin raina sana’a hakan zai zama silar samun arziki ga matasanmu , ta wannan tafarkin duk za mu tsira mu kuma samu aminci a cikin rayuwarmu.

Kamal Alkasim ya rubuto daga Kano

Imel: [email protected]