Airtel Afirka ta yi sabon shugaba

 Daga AMINA YUSUF ALI

Airtel Afirka ta ba da sanarwar ritayar  Babban Jami’in Zartaswarsa, Olusegun Ogunsanya, wanda zai akiye aiki a ranar 1 ga Yuli, 2024.

Ogunsanya, ya fara aiki da kamfanin  Airtel a shekarar  2012, shi yake kula da harkokin sadarwa na Nijeriya da kamfanin hada-hadar kudi na tsahon shekaru tara kafin a yi masa nadin  Babban Jami’in Zartaswar rukunin kamfanonin a cikin shekarar 2021.

Saboda saninsa da yadda Afirka take da gidewarsa waen rarraba kaya a cikinta, ya kasance a lokacin da yake shugabantar kamfanin ya samar da bunkasar kudin shiga masu tarin yawa tsahon shekaru, sannan ya samar da sababbin abubuwa da dama don amfanin kwastomomi a fadin nahiyar gabadaya. 

Airtel, a jawabinsa ya bayyana cewa, saboda irin gagarumar gudunmowar da ya ba wa kamfanin a yayin da yake shugabantar sa, da kuma saninsa sosai da nahiyar Afirka, Ogunsanya shi me zai zama Shugaban kaddamar da Gidauniyar Taimako ta Airtel Afirka.

Kamfanin ya kara da cewa, wannan gidauniya za ta fi mai da hankali a kan b ada taimako na dijital, taimakon kudi, tallafin ilimi da kare muhalli daga gurbata. Kuma ita gidauniyar zaman kanta za ta yi ba tare da ta jingina da rukunin kamfanoni na Airtel Afirka ba.

Duk da ritayar tasa, Ogunsanya zai cigaba da zama mai ba da shawara ga sabon Babban Jami’in Zartaswa har na tsahon watanni 12.

Hakazalika, kamfanin ya kuma sanar da nadin Sunil Taldar a matsayin Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Zartaswarsa wanda zai gaji Ogunsanya bayan ritayarsa.

Taldar, shi ma ya fara aiki da Airtel Afirka a watan Oktoba na 2023. Kuma zai fara aikinsa a matsayin Shugaban ranar 1 ga Yuli ranar da shi kuma Ogunsanya zai sauka.

Haka kuma kamfanin ya gode wa Ogunsanya irin kokarinsa da jajircewsrsa a lokacin da yake hugabantar reshen na Afirka. Kuma ya nuna jin dadinsa yadda Ogansanya ya amsa tayin kamfanin na zama shugaban Gidauniyar ba da taimako ta kamfanin.