Daga BASHIR ISAH
Matasan Arewa sun jinjina wa Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa, dangane da kokarin da yake yi wajen kare rayukan ‘yan kasa da kuma dukiyar gwamnati.
Matasan sun yi wannan yabo ne ta bakin kungiyarsu ta Northern Youths Association of Nigeria (NYAN) cikin wata sanarwar manema labarai da kungiyar ta fitar ranar Asabar a Bauchi.
Matasan sun ce, “Mun yaba da kokari da jajircewarsa wajen maido da zaman lafiya a Nijeriya. Hakika ya dora rundunar sojin Nijeriya kan turbar da ta dace.
Shugaban kungiyar, Ambasada Godiya T. Adams Bogoro, ya bayyana cewa, bayan nazari da lura, “Muna da yakinin CDS ya yi wa nauyin da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya dora masa adalci.”
Ya kara da cewa, kokarin da Janaral Musa ya yi wajen yaki da ‘yan fashin daji da IPOB, ya sanya kungiyar bayyana kwarin gwiwarta a kansa.
“Mun yaba da ingantattun dabarun da CDS ya dabbaka tare da hada hannu da sauran hukumomin tsaro wajen yaki da matsalolin tsaron kasa,” in ji Bogoro.
