Za a daƙile layukan Glo daga barin kiran MTN saboda rashin biyan haraji – NCC

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Kula da Kafafen Sadarwa ta Nijeriya (NCC), ta bayyana cewa akwai yiwuwar masu amfani da layin sadarwa na kamfanin Globacom su fuskanci kwarya-kwaryar dakikewa wajen kiran layukan sadarwa na kamfanin MTN.

Hukumar ta bayyana haka ne a sanarwar da ta fitar ran Litinin wadda ta samu sa hannun Daraktan Sashen Hulda da Jama’a, Reuben Muoka.

NCC ta ce za a fuskanci hakan ne biyo bayan rashin biyan harajin sadarwa daga bagaren Globacom.

Hukumar ta kara da cewa ta ba da izinin a katse sadarwar kamfanin Globacom daga MTN Nigeria Communications Plc.

A cewar Hukumar, “An sanar da Globacom buƙatar da kamfanin MTN ya gabatar kuma an bai wa kamfanin (Globacom) damar fadin albarkacin bakinsa da kuma bayyana matsayinsa.

“Hukumar ta yi nazarin bukatar da aka gabatar da kuma badakalar da ke kewaye da batun inda ta gano lallai Globacom ba shi da isassu kuma gamsassun hujjoji na rashin biyan harajin da ke kansa.

Sanarwar ta NCC ta kara da cewa, bayan karewar wa’adin kwana 10 daga ranar da aka ba da sanarwar, muddin kamfanin Globacom bai yi abin da ya kamata ba to, masu amfani da layin sadarwar na kamfanin ba za su iya ci gaba da kiran layukan MTN da layinsu ba, amma za su iya amsa kira.