Tinubu ya dakatar da Ministar Jinƙai, Betta Edu kan zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayar da umarni kan a dakatar da Ministar Jinkai da Yaki da Talauci, Dokta Betta Edu daga mukaminta na minista.

Kuma dakatarwar ta fara aiki ne nan take, kamar yadda Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Ajuri Ngelale ya sanar a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce Tinubu ya dakatar da Betta ne domin kare mutuncin gwamnatin kasa da kuma aiki da gaskiya.

Ta kara da cewa, Tinubu ya bai wa Shugaban EFCC umarni kan gudanar da cikakken bincike a kan Betta bisa zargin da ake yi mata na karkatar da wasu makudan kuaden gwamnati.