Dandalin shawara: Mijina ya nisanta kansa da zama uban cikin da ke jikina

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Aisha Asas barkanki da yau. Ya jama’a dai. To madalla. Don Allah ki taimaka min yadda ki ka saba ba wa mutane shawara da suke amfana da ita har ta yi masu aiki ga abinda yake ta damun rayuwarsu.

Kina ji na ko, wato miji ne nake tare da shi da ban san kowanne irin mutum ne ba, ya sani duk daren Allah sai ya………..(mun cire kalmomin saboda rashin dacewar ta). Kuma kar ki ce sau daya, har ba iyaka. To wai yanzu na yi ciki, asibiti an ce Ina dauke da juna biyu na wata biyar, amma mijin nawa ya ce shi bai san zancen ba, wai wallahi ba cikin sa ba ne.

Sai fada yake yi wai tun kan ya aure ni ma Ina ba shi yana……………, don haka ya san ko da can ba shi kadai ba ne bare yanzu. Shi lallai ba zai amshi cikin ba.

Ki ba ni shawara yadda zan kwaci ‘yancina kan wannan tozarci da mijina ke shirin yi min don Allah. Na gode sosai da sosai.

AMSA:

Da farko dai ‘yar’uwa zan fara da ba ki shawara kan irin yadda ki ke jan zaren kalaman da ki ke yi. Idan kin karanta yadda muka tsara tambayar da ki ka turo za ki fahimci cewa, mun katse kaso mai yawa daga irin furucin da ki ka yi, kuma mun canza wasu daga cikin kalmomin da ki ka yi amfani da su.

Ki sani, ko a kalamai kawai ana iya fassara mutum, domin ba ya daga cikin halayyar mutumin kirki amfani da kalaman batsa, ko fadar wasu ababe da aka sakaya a yadda suke. Ba wayewa ba ce fadar irin kalaman da ki ka yi amfani da su, asalima ni na fi kallon shi a matsayin jahilci.

Idan za mu fara warware wannan matsala taki, za mu soma ne da zancen da ki ka yi na karshe, wato amincewa da ki ka yi da mijinki tun kan ya aure ki. A wannan ne matsalar ki ta samo asali da tushen ta.

Yayin da ku ke ganin wayewa ce ko tsananin soyayya ce mace ta bada kanta ga namijin da za ta aura tun kan ta zama matarsa, wannan wayewar ko soyayya ce za ta zama mashi yayin da ku ka aikata wannan varna, wanda mashin zai vurma lafiyayyen auren da ku ka yi tun a lokacin da aka daura shi. Domin zai dasa zargi a tsakanin ku.

Kowanne daga cikinku na zargin dan’uwansa da abinda ba wai ya kama shi yana yi da wani ba, sai don kun aikata a lokacin da ya haramta gare ku.

Shi kuwa zargi idan ya samu wurin zama a aure, to sunan auren tashin hankali. Wannan ne ummul khaba’isin matsalar da ki ke fuskanta a yanzu. Ba wai rashin fahimta ko rashin hankali ne tare da mijinki ba kamar yadda ki ke ikirari.

Ta yaya namijin da ya nemi ki ba shi kanki kina gidanku, yana matsayin ajnabin ki, wanda aure bai shiga tsakaninku ba, kuma ki amince masa bayan kina da damar hana shi, ya kuwa za a yi ba zai dinga zarginki ba? Shi fa ya nema ne, kuma kina da damar ki, amma ki ka amince, to ya zai iya aminta da cewa shi kadai ne babu wasu irin sa?

Ita fa dokar Allah kowacce iri ce alfanun ta gare mu yake. Kin bin ta kuwa na tattare da matsalolin da tabbas za mu yi nadamar jawo wa kanmu su.

Sai matsalar musanta zama wanda ya yi ma ki ciki kuwa mai sauqi ce idan ki ka duba cigaba da zamani ya zo da shi, wato za a iya gwaji na DNA don gane gaskiyar uban cikin. Sai dai me Musulunci ya ce game da irin wannan matsala idan ta taso?

Za mu ci gaba a mako mai zuwa.