Tinubu ya tsige manyan jami’an gwamnati guda biyu

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya tsige Mataimakin Shugaban  hukumar kare hakkin masu amfani da kayayyaki da aka fi sani da FCCPC a takaice, Mr. Babatunde Irukera.

Kazalika, Tinubu ya tsige Babban Daraktan Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati (BPE), Mr. Alexander Okoh.

Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Chief Ajuri Ngelale ne ya bayyana tsigewar cikin sanarwar da ya fitar  jiya Litinin, inda ya ce matakin tigewar ya fara aiki ne nan take.

Sanarwar ta kara da cewa, an umarci jami’an da lamarin ya shafa da su mika ragamar gudanar da ofisoshinsu ga jami’i mafi girma a bakin aiki a ma’aikatarsu kafin lokacin da za a nada wadanda za su maye gurbinsu.

Haka nan, ta ce Tinubu ya dauki wannan mataki ne a matsayin bangare na kokarin da yake na neman inganta muhimman ma’aikatu da kuma karfafa tattalin arzikin kasa.