An ɗaura auren jarumin Kannywood Abdullahi Amdaz, a Maiduguri

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano

A yanzu haka dai ta tabbata jarumin Kannywood Abdullahi Amdaz ya zama mai igiya biyu.

Amdaz ya kara aure a ranar Asabar, 30 ga Disamba, 2023 a garin Maiduguri, Jihar Barno

An daura auren Abdullahi Amdaz da abar kaunar sa A’isha Umar Timta da misalin karfe 11:00 na safe a gidan sarkin Gwoza da ke kan Titin Gombale, kusa da makarantar Capital, Giwa Barrack, Maiduguri, Jihar Barno.

Allah ya ba su zaman lafiya da zuria dayyiba.

By Editor