Yadda sabon bidiyon waƙar ‘Tarko’ ke haskawa a Masana’antar Kannywood

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano

Kamfanin Bee Safana production Place ya fito da wani sabon Bidiyon waka mai suna ‘Tarko’, wanda fitaccen jarumi a masana’antar Kannywood Daddy Hikima (Abale) da fitacciyar jaruma mai haskawa Bilkisu Bee Safana suka fito a ciki.

Wakar wacce ta fito da sabon salo mai ban sha’awa ta samu karbuwa kuma tana kan samu a daidai wannan lokaci. Bidiyon wakar ya nuna yadda wani azzalumin shugaba ke kama wata budurwa (Bee Safana) ya daddaureta da igiya yayin da shi kuma masoyinta (Abale) ya ke zuwa yana arangama da wadannan mutanen don ganin ya kwato masoyiyar tasa, amma duk a cikin wake.

Ta cikin baitukan wakar Bee Safana na cewa, ‘Tarko na shiga ga ni nan cikin ukuba… Duk tsananin wuya.. zuciya ba wani kai ne’.
Shi kuma kuma Daddy Hikima zai ce, ‘A ina kike?’ Sai su kuma suna cewa.. yarku.. yarku
Sai shi Daddy Hikima ya ce, ‘ga ni nan zuwa gareki in ban ganki ba… rayuwata ba sukuni…sai ya kara da cewa… a ina kike? Sai ta ce..Gani nan cikin ukuba..

Jurumar hakika ta taka rawar ban mamaki, ganin irin yadda aka daddaureta da igiya a wakar, wanda wannan ba kowacce jaruma ba ce za ta iya hakan.

Babban darakta a Masana’antar Kannywood wanda shi ne furodusan wakar Kamilu Ibrahim Dan Hausa ya bayyana cewa, abubuwa uku ne suka sanya wakar farin jini inda ya ce:

“Abu na farko shi ne mun yi amfani da salo wanda ba a saba gani ba a Kannywood wanda wasu ma da dama gudun sa suke, na biyu mun yi amfani da jarumai da ake yayi, wato Daddy Hikima da aka fi sani da Abale, da kuma jarumar waqar Bilkisu Bee Safana da take tashe a yanzu.

Sai abu na uku shi ne mun samar da mutane 500 da suka fito a wakar, sannan muka samu kwararru da suka gina mana alqarya, inda za a ga cewa wani azzalumin shugaba ne yake kama karya yake garkuwa da mutane da amfani da miyagun kwayoyi duka dai don masu kallo su nishadantu. To wannan ya sa wakar ta samu karvuwa a cikin al’umma.”

Bidiyon wakar wanda ya fito a yan kwanakin nan na sabuwar shekarar 2024 za a iya kallonsa a kafar YouTube da kuma shafin Daddy Hikima YouTube.

By Editor