DAGA MUKHTAR YAKUBU.
Darakta Kamal S. Alkali da amaryar sa Jaruma Hauwa S. Garba sun samu karuwar haihuwar da namiji wanda aka radawa suna Ahmad.
A ranar 23 ga Disambar shekarar da ta gabata 2023 ne aka yi haihuwar a wani asibiti mai zaman kansa a cikin garin Kano.
Cikin murna da jin dadi, Kamal S Alkali, ya bayyana godiyar sa ga Allah da ya nuna masa wannan lokaci da matar sa Hauwa S Garba ta yi wannan haihuwar bayan wata 10 da auren su. Domin kuwa an daura masu aure ne a watan Maris din da ya gabata wanda a cikin wata na 10 Allah ya azurta su da samun wannan karuwa.
Ya kara jadada godiyar sa ga Allah da ya sa ya samu mata ta kirki wadda duk wani abu na burin rayuwa bai dame ta ba. Saboda duk da irin kallon da ake yi wa ‘yan fim musamman mata a kan zamantakewar aure, ita ta zamo ba mai son duniya ba da har ta zabi zaman auren.
Don haka ne suke zama lafiya da juna da kuma fahimtar juna. Don haka ya yi fatan Allah ya kara musu zaman lafiya a tsakanin su da ita da uwargida, ya zama zaman lafiya cikin aminci.
