Da Ɗumi-ɗumi: Nijar, Burkina Faso, Mali sun yi adabo da ECOWAS

Daga BASHIR ISAH

Kasashen Burkina Faso da Mali da Nija sun sanar da ficewarsu daga Kungiyar Bunkasa Tattalin Azrzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).

Shugabannin kasashen yankin Sahel ukun sun fitar da wata sanarwa inda suka ce “shawara ce mai cikakken iko” ta barin kungiyar “ba tare da bata lokaci ba”.

Kasashen masu fama da matsalolin tsaro dtun bayan da sjoji suka karbe mulkin kasashen.

Idan dai za a iya tunawa, a watan Yulin Bara ne sojoji suka yi juyin mulki a Nijar, haka ma Burkina Faso 2022, sai kuma Mali a 2020.

Duaka kasashen uku ECOWAS ta takatar da su daga kungiyar, yayin da Nijar da Mali suka fuskanci takunkumai daban-daban.