Rundunar Soja ta yi wasan shekare-shekara a Gusau

*T yi alkawarin kara kokarin kawo karshen ‘yan bindiga a Zamfara.

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Rundunar Sojan NIjeriya ta 1 Brigade Gusau a Jihar Zamfara, ta gudanar da bikin African Social Activities WASA na shekara-shekara domin gudanar da ayyukanta a shekarar 2024 da nufin kara kaimi wajen yaki da ‘yan bindiga a jihar ta Zamfara.

A jawabin maraba, Birgediya Janar 1 Brigade, S. Ahmed wanda ya samu wakilcin Kanar J. Umaru a wajen bikin da aka gudanar a 1 Brigade Command Gusau a ranar Asabar ya bayyana cewa an fara bikin na WASA ne a shekarar 1901 da nufin samar da hadin kai tsakanin sojojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro.

A cewarsa, rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ karkashin rundunarsa ta ta taka rawar gani wajen magance matsalar ‘yantadda da sauran miyagun laifuka a jihar ta Zamfara.

“Rundunar Hadarin Daji ta hallaka ‘yan bindiga da dama a wasu yankunan jihar Zamfara domin dawo da zaman lafiya a jihar”.

Ya bukaci al’umma da su kai rahoton duk wani bakin haure da basu yarda dasuba ga rundunarshi domin daukar matakin gaggawa.

Brigr. S. Ahmed ya bayyana cewa rundunar sojojin Najeriya 1 Brigade a jihar zata cigaba da jajircewa wajen yakar ‘yan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka a jihar har sai an samu zaman lafiya a jihar.

Ya kuma Yi Kiran ga sauran jami’an tsaro a jihar da su baiwa rundunar da ke karkashin sa hadin kai domin su yi aiki cikin lumana domin shawo kan matsalar rashin tsaro sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda a jihar.

A nasa jawabin gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal wanda ya samu wakilcin mai martaba sarkin Kaura Namoda Alh. Muhammad Sanusi a wajen taron ya bayyana cewa gwamnatin sa ta kafa tare da bayar da gudunmawa sosai wajen daukar ma’aikata da horas da jami’an kare hakkin jama’a da za su yi aiki a matsayin masu yawan karfi a jihar.

A cewarsa, Jami’an tsaro na al’umma za su tallafa wa gine-ginen tsaro na gargajiya da nufin dakile duk wani nau’in fashi da makami da garkuwa da mutane da satar shanu da sauran miyagun laifuka a jihar.

“Haka zalika gwamnatin jihar ta yi kokarin yin amfani da fasahar zamani wajen inganta tsaro a jihar yayin da ake sanya na’urar daukar hoto a wasu muhimman wurare a jihar Zamfara domin taimakawa jami’an tsaro wajen sa ido kan ayyukan da suka saba wa doka da nufin inganta tsaro a duk fadin jihar. kasar,” in ji Gwamna Dauda.

Gwamnan ya kuma yabawa hafsoshi da sojoji na 1 Brigade da Operation HADARIN DAJI a jihar Zamfara bisa kwarewa da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Zamfara.