Gwamnatin Zamfara ta ƙaryata rahotannin da ake zargin ɗan PDP na kai wa ‘yan bindiga makamai

Daga Sanusi Muhammad, a Gusau

Gwamnatin Jihar Zamfara ta karyata rahotannin baya-bayan nan da wasu kafafen yada labarai suka rika yadawa cewa an kama daya daga cikin shugaban jam’iyyar PDP  da hannu kan badakalar kai wa ‘yan bindiga makamai a jihar.

Mai ba wa Gwamna shawara kan harkokin siyasa ga Gwamna Dauda Lawal, Hon.  Yahaya Yari, ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a ranar Laraba a ofishinsa.

Yari ya bayyana rahotannin a matsayin na sharri da rashin tushe balle makama, yana mai bayyana hakan a matsayin siyasa ce da yarfe daga wasu tsirarun mutane.

“Zan iya bayyanawa karara cewa wanda ake zargin da sojoji suka kama da bayar da makamai da alburusai ga ‘yan bindiga ba shi da katin zama dan jamiyyar PDP , don haka gwamnatin jihar ta dauki rahotannin a matsayin soki-burutsu da kuma yunkurin wasu mutane na bata wa gwamnati suna,” a cewar  Yari.

Ya kuma yi kira ga ma’abuta yada labarai a jihar da su rika tantance bayanansu a ko da yaushe kafin su buga .

“Muna kira ga ‘yan jarida da su yi watsi da duk wani bayani da ba shi da tushe a cikin rahotonsu domin a kullum Gwamnatin Jihar karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta himmatu wajen ganin ta ceto Zamfara daga dukkan komabaya.”

Hon.  Yari ya bukaci mutanen jihar da su rika bai wa gwamnatin jihar goyon baya a kodayaushe a kokarin da take na mayar da jihar zuwa matsayi mafi girma.

 “Muna kira ga al’ummar jihar nan da su kwantar da hankulansu tare da mara wa gwamnati baya a karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal a yunkurinsa na ceto jihar daga rashin tsaro da sauran koma bayan tattalin arziki.”