Akwai buƙatar malamai su duba lamarin walimar sauka da ake yi yanzu

Daga SALIHA ABUBAKAR ABDULLAHI, Zariya

A zamanin dauri duk lokacin da iyaye suka ga ‘ya’yansu sun kusa sauke Alkur’ani mai girma zuciyarsu kan cika da murna da farin ciki ne tare da fatan Ubangiji ya nuna musu lokacin.

Idan ranar ta taho masu aka tabbatar da hakan, iyaye kan bi malamai da kyautar da ba ta taka kara ta karya ba don nuna godiya ga malaman da kara musu kwarin gwiwa domin su kara jajircewa kan abinda suke yi, su kuma su karva suna farin ciki da matukar godiyar karamcin da iyayen yara suka nuna musu.

Idan makarantar allo ce, tsananin iyaye su dafa shinkafa da wake, a zuba mangyada da yaji, wasu iyayen zasu sai waina/masa ne da kosai, wasu kuwa wainar kadai za a badawa kulli-kulli ko sikari a kai makaranta domin rabawa dalibai/almajiran sadaka.

Abin lura, duk hakan na faruwa ne bisa amincewa da son aikatawa daga iyayen, ba wai malaman ne gindaya masu sharadi, ko yanke irin abinda za su iya kawo wa a rana irin wannan ba.

Sabanin wannan zamani da muke ciki yanzun wanda tashin hankali da damuwa ke dabaibaye iyaye, ‘yan’uwa da abokan arziki dalilin sabbin tsurfa da aka kutso dasu don nuna murna.

Babban abin takaici mutane sun mai da al’amarin sauka ko haddar da ‘ya’yansu ke yi tamkar gasa wanda ya karade ko’ina ya zama ruwan dare gama duniya.

Da zarar Makarantun Islamiyya sun fara shelar kaddamar da walimar sauka ko haddar dalibai, tsugune ba ta qare wa iyaye ba saboda shirin gagarumin buki ya tashi kenan domin kokarin nuna wata bajinta.

Daga wannan lokacin iyaye za su fara shigi da ficin neman kudade na shirin gagarumin bukin.

Ga masu hannu da shuni ba matsala ce ba domin da yawa iyaye kan ninka fiye da abinda malamai suka nema domin tafiyar da walimar, yayinda iyaye talakawa ko kuma marayu kan hada da cin bashi, ko zubin adashe na musamman wai domin a fitar da yaro ko yarinya kunya cikin ‘yan’uwa dalibai.

Bayan nau’ikan abincin da ake dafawa kala-kala, za a sayi lemunka sha, a hada da su zobo da kunun aya, naman kaza ba a maganarsa domin akwai makarantun da ke saka dokar dole kowanne dalibi/daliba su kai wa malami sadakar gasassa ko soyayyiyar kaza na wasa makoshi, bayan tsire ko naman rago da shanu.

Kayan da ake sarrafawa da fulowa kuwa su ba a iya kididdige nau’insu, tun daga donut, samosa, cake da sauransu. Al’amarin zallla hauka.

Bayan abincin kuma sai batun ankon da dalibai za su saka ranar walimar banda kudin da aka kididdige kowanne dalibi zai bayar na Allon Zayyana da takardar shaida.

Bayan an gama da hidimar cikin makaranta kuma sai iyaye su dawo na hidimar jama’a da zasu tara cikin gidajensu ‘yan taya murna, inda nan ma yawanci wani gagarumin bukin ne za a shirya.

Idan mata ne suka sauke su sha kwalliya tamkar ta amare, su taho su zauna, a ci a sha sannan a mika wa jama’ar da suka taru kayan rabon da iyayen suka sake kashe kudi suka yi wadanda suka kunshi; littafan rubutu, littafan adduo’i, alkalamai, hankici, kalandoji masu dauke da hotunan dalibi ko daliban, da sauransu.

Wani taron idan ka gani kai ka ce bukin aure ake yi, sai in ka ga ba ya dauke da shaidar bukin da ake yi zaka fahimta.

Ya jama’a wane irin rayuwa ce muka daukarwa kanmu? Yayinda masu hannu da shuni ke da kudin yin abinda suka ga dama da kudadensu, kai talaka fa?

A cikin wannan lokacin da miliyoyin mutane ke wayar gari ba abinda zasu ci, da dama wasu sun kwana sun yini ba su samu saka komi a bakin salati ba, idan sun samu kuma sai dai a lasa a hakura ba don an koshi ba, wadanda suka samu taimakon Allah ne za su ci sau daya ko biyu a rana amma a yini guda sai a dafa abincin da akalla za a iya kwanaki biyu zuwa uku ana ci a koshi.

Da yawan mutane na shiga cikin halin kaka ni kayi a dalilin wannan bidi’ar da muka bullowa kanmu dashi da rana tsaka.

Ba a hana sadaka ba, ba a hana nuna murnar yaranmu sun taka wani matakin karatu na addini ba amma wacce irin tsabtacciyar hanya ya dace ayi wannan murnar?

A tunanina tunda a na yin karatun domin Allah ne da fatan samun tsira da ilmin addininmu bai kamata a mai da al’amarin ya zama bukin da aka kutso riya cikinsa ba, wanda har ya kan zama abin gori ko shaguve ga daliban da iyayensu ba su da karfin kwatanta wannan bidi’ar.

Jama’a ku sani akwai ‘yan mata da yawa da suke shiga hatsarurrukan haduwa da lalatattun maza musamman yaran da iyayensu ba su da karfin sauke wannan nauyin na hidimar walima, inda mazan kanyi amfani da wannan raunin su bada kudin a matsayin fansar mutuncinsu.

Al’amurran na neman zarce tunani wanda idan har mun ci gaba da saka ido aka ci gaba da hakan, ta ya muke tunanin za a samu albarkar karatun da ake nema bayan da kanmu mun gurvata shi mun kutso da wasu bidi’oin da ba mu ji cewan Manzon Tsira ya yi hakan ko anyi hakan a lokacinsa ba ko wasu daga cikin Sahabbansa sun dabbaka shi ko bayan wafatinsa?

Jama’a mu ji tsoron Allah mu rinka kiyayye dokokokin Ubangiji da tsayawa inda aka tsayar damu domin samun tsirar gobe qkiyama da kuma samun haske da albarka a rayuwarmu da ta zuriyyarmu.

Muna addu’ar Ubangiji ya shiryemu gabadaya, ya ci gaba da mana jagoranci kan dukkan al’murranmu da zuriyyarmu bakidaya. Kar ya bar mu da dabarun kanmu.