Rashawa ke hana ganin bayan matsalolin tsaro a Arewacin Nijeriya – Shettima

Daga BASHIR ISAH

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya danganta matsalar tsaron da ta ki ci, ta ki cinyewa a yankin Arewacin Nijeriya da rashawar da ake fama da ita a tsakanin shugabannin al’umma.

Ya bayyana haka ne sa’ilin da yake jawabi a wajen taron lacca da bada lamba karramawa na shekara-shekara karo 10 wanda Gidauniyar Sir Ahmadu Bello ta shirya sannan Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya dauki nauyin gudanarwa.

A jawabin nasa, Shettima ya jaddada yadda rashawa ta yi matukar tasiri wajen zama babban kalubale ga fannin tsaron kasar nan.

Matamakin Shugaban Kasar wanda ya samu wakilicin Mai ba shi Shawara kan Sha’anin Siyasa, Hakeem-Baba Ahmed a wajen taron, ya ce babu yadda shugabanni za su iya kawar da matsalar sace-sace, fashin daji da garguwa da mutane muddin suna ta’ammali da rashawa.

Don haka ya yi kira ga shugabanni da a koma kan turbar nan ta aiki da gaskiya da amana kamar yadda aka gada daga marigayi Sardauna domin cimma daidaito.

A nasa bangaren, Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya karfafa batun Shettima innda ya ce rashawa bababbar kalubale ce ga cigaban kasar nan.  

Don haka shi ma ya yi kira ga shugabanni da su rungumi tsarin yin aiki da gaskiya da amana don samun nasara wajen dakile matsalolin da suke addabar kasa.

Galibin wadanda suka yi jawabi a wajen taron, sun nuna bukatar a koma a yi koyi da magabata irin su Sardauna wajen aiki da amana domin kasa ta yi kyau sannan alumma su ji dadi.