‘Ba mu amince da ficewar Burkina Faso, Mali, Nijar ba’ –  ECOWAS

Daga BASHIR ISAH

Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), ta bayyana cewa har yanzu ba ta samu a hukumace sanarwar ficewar kasashen Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nija daga kungiyar ba, don haka ba ta amince da ficewar da suka ce sun yi daga kungiyar ba.

Cikin sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi, ECOWAS ta ce “tana aiki tukuru tare da wadannan kasashe domin maido da tsarin mulkin dimokradiyya.

“Burkina Faso da Nija da kuma Mali, kasashe ne masu matukar muhimmanci ga Kungiyar, kuma tana ci gaba da kokarin ganin an samu mafita game da tsarin dimokradiyya a cikinsu.”

A ranar Lahadin da ta gabata shugabancin kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar da ke hannu sojojin juyin mulki suka bada sanarwar ficewar kasashen daga kungiyar ta ECOWAS, suna masu cewa kungiyar ta zame wa mambobinta barazana.

Shugabannin kasashen yankin Sahel ukun sun fitar da wata sanarwa inda suka ce “shawara ce mai cikakken iko” da suka yanke a tsakaninsu ta barin kungiyar “ba tare da bata lokaci ba”.

Kasashen masu fama da matsalolin tsaro dtun bayan da sjoji suka karbe mulkin kasashen.

Idan dai za a iya tunawa, a watan Yulin Bara ne sojoji suka yi juyin mulki a Nijar, haka ma Burkina Faso 2022, sai kuma Mali a 2020.

Duaka kasashen uku ECOWAS ta takatar da su daga kungiyar, yayin da Nijar da Mali suka fuskanci takunkumai daban-daban.