Ashe ɓarayin mutane sun shigo Abuja?

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Da shigowa Abuja dan Nijeriya zai san ya shigo birnin da shugaban kasa ya ke da zama don ganin manyan ofisoshin jami’an tsaro kama daga na soja, ‘yan sanda, jami’an tsaron farar hula da sauarn su. Ga mutane masu wutar jiniya na zirga-zirga. Barikoki kadai a bayan fadar shugaban kasa ta Aaso Rock na nuna akwai bambancin tsaro daga sauran yankunan kasa.

Ba lalle ne birnin na da yawan dogayen gine-gine ba amma dai ga dogayen kamarorin tsaro a sassa daban-daban da ko su na aiki ko ba sa yi wannan sai jami’an tsaro ne za su iya bayani. Akalla hakan zai ba wa baki kwanciyar hankali cewa za a iya yawo a ko ina cikin birnin ba tare da fargabar wani mugun iri zai iya kai mu su farmaki ba. A gaskiya ba haka lamarin ya ke ba don kwazazzabon tsakiyar birnin kadai ma na dauke da wasu miyagun matasa da kan fizge waya ko jaka daga hannun mutane su yi kundunbala su bace a karkashin gadojin da ko da wasa mutum mai hankali ba zai so shiga ba. Kalubalen fasa mota don sace ta ko kayan da ke ciki ba wani sabon abu ba ne.

 Barayi ko ‘yan fashi ma kan iya fakon mutum sai ya fito daga motar sa su kai ma sa cafka don lale ma sa kayan alijihu da ma awun gaba da motar sa. Na tava samun labarin barayin sun taba shiga wani shagon magani a anguwar Wuse 2 da daren bai yi nisa ba su ka tsare mutanen da su ka zo sayen magani su ka amshe kudin su da na shagon maganin su ka gama komai ba tare da masu wucewa ta kan titi sun sani ba.Wani lokaci ina aiki na a ofishi na da ke anguwar Utako sai Umar Gombe na gidan talabijin na Kaftan ya kawo min ziyara, bayan mun yi sallama ya fice ya tsallaka titi sai ya ci karo da barayi.

A nan su ka murde shi su ka kwace ma sa duk abubuwa masu amfani da ya ke tare da su a lokacin. Wannan fa ya afku ne kan titin nan da ya nufi anguwar Maitama daga gadar nan ta Bega. Ni kai na na tava sha da kyar a wata shekara yayin da na tsaya don shiga shagon sayar da magani a nan Uktako yamma da kwanar tashar mota ta Utako.

Fita ta daga mota ke da wuta sai wasu matasa kimanin 4 su ka kawo min wafta daya daga cikin su na cewa “I WILL SHHOT YOU!” wato ma’ana zan harbe ka in ka yi kokarin yin wani abu na tsira. Ya nuno ni da wani abu mai kama da karamar bindiga. Gaskiya ban razana ba don nan take na danna na’urar jikin mabudin motar inda mota ta rufe kirib daga nan na sunkuya don kaucewa damkar mugun irin zura da gudu su ma matasan su ka rufa min baya.

Bayan na yi nisa ba tare da samun taimakon kowa ba sai na tsaya don na lura matasan sun ga ba nasara don haka sun shige lunguna. Sabon labarin shi ne na masu satar mutane don karvar kudin fansa wanda ya yi kaurin suna kwanan nan bayan sace yara mata kimanin 6 da wasu mutane a yankin karamar hukumar Bwari. Rashin hada Naira miliyan 60 kamar yadda rahoto ya nuna miyagun su ka kashe daya daga ‘yan matan mai suna Nabeeha don firgita mahaifin su Kadriyar ya dage wajen samo kudin fansar. Hakika duk da nasarar kubutar sauran yara matan hakan bai goge juyayin rashin Nabeeha ba wacce ke daf da kammala karatun jami’a.

Masu sharhi na ganin zai yi wuya a ce wadanda ke satar mutane a yankunan kananan hukumomin Abuja masu makwabtaka da dazuka Za su zama kuma su ne masu shigowa har cikin gari su aikata irin wannan mummunan aikin.

 Dama hawa babur haramun ne a cikin kokuwar Abuja don haka duk wadanda za su yi satar sai dai su zo da mota ko kuma su kwace motar wanda za su sacen. Wani labari ya tabbatar da sace wani mutum a layin gidan mai yayin da ya ke cikin motar sa kirar HILUX inda barayin su ka shiga motar su ka tilasta shi ya bi umurnin su da hakan ya sa su ka fice da shi har jihar Katsina. Irin wannan fargaba ya sa wasu kan kulle motar sa daga ciki in su na wajajen da su ke fargabar yiwuwar samun miyagun iri. Karamar Hukumar Karu a jihar Nasarawa da ke jikin Abuja ma na zama bigiren da a ke samun matsalar satar mutane.

Shugaban karamar hukumar James B. Thomas wanda har ya taba kaddamar da dokar hana yawon dare a yankin don labarin kaurowar ’yan ta’adda, ya ce a na cigaba da daukar matakai amma a kashin gaskiya har yanzu fargabar na nan. Thomas ya ce karamar hukumar na kunshe da kusan jama’ar kowane yanki na Nijeriya don haka ba mamaki a iya samun miyagun iri. Ba kalubalen satar mutane ne kadai matsalar yankin ba, har da yara matsafa da a ke zargi da arangama da juna da kan haddasa asarar rayuka.

Za ku iya tunawa da wani faifan bidiyo na cin amana da ya yi yawo na wata mata a yankin Karu daga anguwar Masaka wacce ta yaudari kawar ta ta kai ga wajen barayin mutane su ka kashe ta inda ita kuma ta dawo ta nemi mallake dukiyar marigayiyar kafin asirin ta ya tonu. Labaru dai na ban takaici da mamaki ba birni ba kauye ba.

Hakika sanennen batu cewa a duk lokacin da a ka samu kuncin talauci to miyagun laifuka za su karu. Rashin karatu ko sana’ar samun dogaro da kai musamman tsakanin matasa na kawo barazanar afkawar su miyagun laifuka da shan miyagun kwayoyi. Idan mutane ba sa zaune cikin salama ko da ba su da kudi ai an samu babbar matsala.

 Wasu bayanan kuwa ba za mu iya bayyanawa ba don za su iya zama gaskiya ko kuma ba su da inganci kan yadda a ke samun tabarbarewar tsaro a dalilan makarkashiya ko cimma wasu muradu. Hatta gwamnati ko jami’an tsaro ba su zurfafa bayanai kan yadda tsaron ya ke da nuna cewa fayyace komai ka iya kawo cikas a aikin samar da tsaron. Marigayi tsohon mai ba da shawara kan tsaro Janar Andrew Azazi ya taba fitowa karara ya aza alhakin ta’addanci kan wasu da ya dace a ce a lokacin su ke yakar ta’addancin. Abun tsoro ne ya zama mai dokar barci ya buge da gyangyadi.

Tsohon kwamandan rundunar soja a Kaduna Manjo Janar Danjuma Ali Keffi mai ritaya ya nuna kokonto yadda a ka yi hatsarin jirgin saman da ya yi sanadiyyar mutuwar tsohon babban hafsan sojan kasa Janar Ibrahim Attahiru.

In za a tuna a 2021 Janar Attahiru da tawagar sa sun rasa ran su a hatsarin jirgin sama a daf da filin saukar jiragen sama na Kaduna.

Ali Keffi a labarin da jaridar yanar gzio ta Premium Times ta wallafa, ya zargi yiwuwar makarkashiyar kashe Attahiru kan masu daukar nauyin ‘yan ta’adda da ke ciki da wajen rundunar sojan Nijeriya.

A bayanan Manjo Janar Danjuma Keffi wanda ya ce an daure shi da yi ma sa ritayar dole; akwai tambayoyi da yawa kan yadda jirgin da ke dauke da Attahiru ya yi hatsari.

Wasu dalilan da Keffi ya bayar akwai jinkirta lokacin tashin jirgin daga Abuja, tashin jirgin daidai lokacin da gagarumin hadari ya taso a Kaduna, saukar jirgin a filin jirgin saman farar hula maimakon na soja da sauarn su.

Hakanan Keffi ya ce a daidai inda jirgin ya fadi ba a samu tonon wani rami ba kamar yadda in jirgi kenan ya fadi, wanda ke nuna jirgin ya riga ya tarwatse tun daga sama kafin sulmuyowa kasa.

Kazalika Keffi ya ce sun tsinci gawawwakin marigayan a gefe can da inda jirgin ya ke kuma an same su a babbake.

Ba mamaki abun da ya fi ba wa Keffi takaici shi ne yadda ya yi ikirarin bayan daure shi ko tsare shi da a ka yi na kimanin kwana 60 tsohon shugaba Buhari bai yi yunkurin ceto shi ba.

Keffi ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya duba kadun abun da ya same shi da binciko fayel din yadda jirgin Attahiru ya yi hatsari.

Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya ba da amincewar gaggawa don odar na’urorin tsaro.

Wike na magana ne a taron ganawa da manema labaru na farko da ya gudanar a sabuwar shekarar nan ta 2024.

Wike ya ce shugaba Tinubu ya amince ba da wani jinkiri ba a samar da na’urorin don taimakawa aiyukan jami’an tsaro wajen yaki da masu satar mutane da sauran miyagun iri.

Ministan ya ce da zarar an kafa na’urorin za a iya ganin miyagun irin da kuma yadda jami’an tsaro za su bi sawun su inda su ka maqale a birnin.

Hakika wasu mazauna Abuja musamman masu hannu da shuni na nuna fargaba kan yiwuwar sace su inda akasari talakawa ke gudanar da harkokin su kamar ba labarin komai na tavarvarewar tsaro.

KAMMALAWA

Yayin da ya ke hakkin gwamnati ne samar da tsaron rayuka da dukiyar al’umma; su ma al’ummar bai kamata su zauna ba tare da duba dama da hagu ba. Babbar shawara it ace tsayawa da addu’a da har kullum ta kan zama makamin Bawa.