Gwamnati ta yunƙura don kwantar wa ‘yan ƙasa da hankali kan ɗauke FAAN, CBN zuwa Legas

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta yunkura domin kwantar da hankalun ‘yan kasa kan batun wasu bangarorin CBN da babban ofishin FAAN zuwa Legas.

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi.

Idris ya bayyana cewa batun dauke wasu hukumomi daga Abuja zuwa Legas ba shi da wata alaka da siyasa.

Idris ya ce, “Duk da cewa muna tunkarar kalubalenmu cikin gaggawa da sadaukarwa, ya zama dole mu tunatar da daukacin ‘yan Nijeriya bukatar tinkarar labaran da ake yadawa ba daidai ba da rarraba kan jama’a.

“Alal misali, ba gaskiya ba ne cewa Dauke Hukumar Kula da Filayen Jirgin Sama ta Kasa (FAAN) da wasu sassan Babban Bankin Nijeriya (CBN) na da daba da manufa ta siyasa.

“Wadannan zarge-zargen ba gaskiya ba ne. Maimakon haka, wannan wani mataki ne na shugabanci domin inganta ayyuka da kuma rage kashe kudin da gwamnati ke yi.”

Kazalika, Idris ya tabi batun kokarin da gamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu na ganin ta magance kalubalan da Nijeriya ke fuskanta da suka hada da matsalolin tattalin arziki da tsaro.

Ya ce gwamnati ba ta ji dadi rikicin da ya sake Kunno kai a Jihar Filato ba, ya ce gwamnati na bai wa ‘yan kasa tabbacin za a binciko tare da hukunta duk wani da aka samu da hannu cikin aukuwar rikicin.

Ya kara da cewa, gwamnati ta samar da shirye-shiryen bada tallafi don rage radadin tsadar rayuwa da suka hada da shirin bai wa dalibai rancen karatu da sauransu, wanda a cewa ya kamata ‘yan kasa su shiga su gajiyar shirye-shirye yadda ya kamata.