Amurka da Birtaniya sun sanar da ƙara wa Hamas sabbin takunkumai sakamakon harin da ƙungiyar ta kai wa Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoban, inda aka samu salwantar rayuka.
Ma’aikatar Baitul Malin Amurka ta ce, wannan matakin ya shafi manyan jami’an da ke ruruta manufar ta’addacin Hamas ta hanyar wakiltar manufofin ƙungiyar a ƙasashen ƙetare tare da kula da asusunta.
Tun bayan harin na Oktoba da ƙungiyar ta ƙaddamar da ya kashe kimanin mutane dubu ɗaya da ɗari biyu, akasarinsu fararen hula, tare da garkuwa da mutane 240, Amurka ke matsin lamba kan mayaƙan.
Baitul Mali Amurka ya ce, Hamas ta ci gaba da dogaro kan gungun wasu jami’ai da aminansu da alamu ke nuna cewa, suna nema wa ƙungiyar tallafin kuɗi don ci gaba da gudanar da ayyukanta a Zirin Gaza.
Takunkuman sun shafi sama da gomman jami’an Hamas da masu taimaka musu da suka haɗa da Isma’il Barhum da ke zauna a Gaza, wanda aka ce shi ne shugaban kula da kuɗaɗe a yankin, inda kuma yake tattaro wa ƙungiyar kuɗin tallafi daga ƙasashen duniya don zuba wa a asusun ma’aikatar kuɗi ta Hamas ɗin.
Birtaniya ta ce, Hamas za ta iya rasa makomarta a Gaza, inda Sakataren Harkokin Wajen Ƙasar, David Cameron ya ce, “takunkuman da aka lafta wa Hamas da mayaƙan jihadi a Falasɗinu za su ci gaba da datse musu hanyoyin samun kuɗaɗen shiga, sannan su zama saniyar ware.”
