Osimhen da Oshoala: ’Yan Nijeriya da suka lashe kyautar gwarazan ‘yan wasan Afirka a 2023

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan wasan tawagar Nijeriya, Victor Osimhen ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon ƙafar Afirka na 2023, inda takwararsa, Asisat Oshoala a ɓangaren ƙwallon ƙafar mata ta zama gwarzuwar ’yar wasan ta Afirka.

Ɗan wasan Super Eagles ya lashe kyautar a bikin da aka gudanar a Marrakech, wanda ya ja ragamar Napoli ta lashe Serie A karon farko bayan shekara 33.

Osimhen ya yi takara tare da ɗan wasan Morocco Achraf Hakimi da na Masar Mohamed Salah.

Ɗan wasan shi ne ya kai Super Eagles gasar kofin Afirka da za a yi a Ivory Coast a baɗi, wanda ya ci ƙwallo 10 a karawar cancantar shiga gasar.

Osimhen ya ci ƙwallo 27 a dukkan fafatawa a Napoli, wadda ta koma kan ganiya a ƙwallon Italiya a kakar 2022-23.

Mai shekara 24 ya zama na farko a Napoli da ya zama kan gaba a cin ƙwallaye a babbar gasar tamaula ta Italiya tun bayan Diego Maradona a 1987/88.

Osimhen ya zama ɗan Nijeriya na farko da ya lashe kyautar tun bayan Kanu Nwankwo a 1999.

Ɗan Ƙwallon na kulob ɗin Napoli mai shekara 24, ya karvi wannan lambar yabo ne a daren Litinin, yayin bikin ba da lambobin karramawa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Aifrka (CAF), inda ya murƙushe hamayyar abokan karawarsa kamar kyaftin ɗin Masar Mohamed Salah da ɗan bayan Moroko Achraf Hakimi.

Kasancewar Osimhen, wanda ya taso a titunan turvaya na unguwar Olusosun cikin birnin Legas, wannan wani cikar burin rayuwa ne bayan ya fuskanci tsananin gargada a lokacin yarintarsa.

“Ina miqa godiyata ga kowa da kowa da ya taimaka mini a wannan tafiya, da kuma duk ‘yan Afirka da suka taimaka wajen ɗora ni kan wannan matsayi duk da matsalolina,” cewar Osimhen.

Osimhen wanda a kullum warin tarin bola yake yi masa sallama a unguwarsu, ya ce yana da maitar burin cimma nasara, duk da ƙalubalen da ya fuskanta a rayuwa.

Sai da ya yi tallan jarida, kuma ya yi sana’ar sayar da ruwan roba, lamarin da ya bayyana da kasancewa a halin rayuwa mafi wahala.

“A matsayina na yaron da ya taso yana talla a tsakanin motoci a kan titi kusan a kullum, don kuvuta daga ɗimbin ƙalubalen da ni da iyayena muka yi fama da shi, zamowa mai irin wannan daraja a Afirka da ma duniyar ƙwallon ƙafa, wani katafaren buri ne a gare ni,” ya rubuta cikin wani saƙo a shafin X.

“Gwagwarmayar ƙwallon ƙafata, ta kasance wani lilo mai hawa da gangara cike da gargada da kuma shauƙi.”

“Cikar buri da murnar nasarori ne suka riƙa yi min ƙaimi, hatta a lokacin da masu suka da nuna ƙiyayya da zafin kaye suka riƙa bugun ƙirjina da ƙarfi.”

Bayan ya ci ƙwallo 26 ne ya taimaka wa Napoli ta lashe gasar Serie A ta farko a cikin shekara 33, Osimhen ya zama ɗan Nijeriya na ɗaya da ya ci lambar karramawa ta CAF a ɓangaren maza tun bayan tsohon ɗan wasan gaban Arsenal, Nwankwo Kanu a 1999.

A fannin mata Asisat Oshoala, ’yar wasan tawagar Nijeriya da Barcelona, ita ce ta lashe gwarzuwar ƙwallon ƙafa ta Afirka ta 2023.

Ta kuma yi takara tare da Thembi Kgatlana (Afirka ta Kudu, Racing Louisville) da kuma Barbara Banda (Zambia, Shanghai Shengli).