Tsadar rayuwa: Ku ƙara haƙuri da lamarin Tinubu, roƙon Malagi ga ‘yan Nijeriya

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan ‘Yan Ƙasa, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya roƙi ‘yan Nijeriya da su ƙara haƙuri da lamarin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu dangane da sabbin tsare-taren da ta fitar da nufin daidaita tattalin arzikin ƙasa.

Malagi ya yi wannan roƙo ne sa’ilin da yake jawabi a wajen taron ƙaddamar da littafi ranar Alhamis a Birnin Tarayya.

Ministan ya yarda cewa lallai ‘yan Nijeriya na fuskantar tasku sakamakon sabbin tsare-tsaren gwamnati, yana mai ccewa gwamnatin na yin abin da take yi ne domin daidaita wa tattalin arzikin ƙasa zama yadda ya kamata.

Ya ce, Shugaban Ƙasa na ci gaba da ƙoƙarin tabbatuwar ƙudirin nan na ‘Renewed Hope Agenda’ da yake da shi domin inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.

Ya ƙara da cewa, tsare-tsare gami da matakan da Tinubu ya ɗauka za su taimaka gaya wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa nan gaba, don haka ya ce ƙudirin “Renewed Hope Agenda” da Shugaba Tinubu ke da shi na kan turbar da ta dace.

By Editor