Nazari: Yadda Gasar Hikayata ta BBC Hausa ke ɗaukaka muryar mata 

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

“Ta dalilin wannan gasa ta Hikayata da BBC Hausa suke shiryawa mata marubuta da a baya ba a san da su ba, yanzu sunan su ya fito. Tabbas gasar tana ɗaga muryar mata ta yadda za su isar da kukansu da bayar da shawarwari na hanyoyin inganta rayuwar mata da zamantakewar al’umma.”

Aisha Adam Hussaini kenan ƴar shekara 27 da ta fito daga Jihar Kano, wacce ta zama gwarzuwa ta ɗaya a Gasar Hikayata ta BBC Hausa ta 2023, yayin da take yabawa da yadda ake gudanar da gasar rubuta gajeren labari ta marubuta mata. 

“Na ji kamar mafarki nake, na kuma ji farinciki marar adadi. Na yi godiya ga Allah da ya sanya ni cikin ukun da suka yi nasara. AlhamdulilLah!”

A cewar Aisha Abdullahi Yabo mai shekaru 30 daga Jihar Zamfara wacce har wa yau ɗiya ce ga babban malamin addinin Musuluncin Sheikh Abdullahi Abubakar Yabo, da ta zo a mataki na biyu a cikin gwarazan marubutan da suka yi nasara cikin gasar Hikayata ta wannan shekara. 

Ita kuwa Aisha Sani Abdullahi mai shekaru 22 daga Jihar Filato wacce ta samu zama na uku a gasar Hikayata cewa ta yi, “Na kasa gasgata labarin da na ji, kamar ba ni ce aka ce labarina ya shiga cikin fitattun labarai uku na gasar Hikayata ba. Gani nake kamar a mafarki, zan tashi a ce ba ni ba ce. Na yi farinciki marar misaltuwa!” 

Waɗannan marubuta mata na daga cikin kimanin marubuta 500 da suka shiga gasar Hikayata da BBC Hausa ke shiryawa duk shekara tun daga 2016, da nufin qarfafa gwiwar mata marubuta da kuma ba su damar bayyana matsalolin da mata a ƙasashen Afirka ke fuskanta, don jawo hankalin hukumomi su ɗauki matakin kawo gyara da inganta rayuwar al’umma.

Yayin da a kowacce shekara ake fitar da gwaraza uku da labaran su suka yi fice a gasar, tare da karrama su da kuma ba su kyautar kuɗaɗe, da nufin tallafawa harkokin su na rubutu. Wani abin ƙayatarwa ma shi ne, akasarin waɗanda suke samun nasara a gasar matasan mata ne, da shekarun su ba su wuce 30 ba. 

Duk shekara gasar Hikayata na ƙara samun karɓuwa sosai, musamman a wajen marubuta mata, waɗanda ke rububin shiga gasar, sakamakon yadda suke kallon gasar a matsayin wani mataki na samun ɗaukaka da shahara a fagen rubutun adabi. Sau 5 Aisha Abdullahi Yabo mai laqabi da Fulani, wacce ta rubuta littafin ‘Fargar Jaji’ ta shiga wannan gasa ta Hikayata, amma bata tava kaiwa ko da matakin farko ba sai a wannan karon Allah Ya nufa.

Ita kuwa Aisha Adam da ake ce wa Ameera, marubuciyar littafin ‘Shu’umar Masarauta,’ ta ce sau biyu ta taba shiga gasar sai a karo na uku ne ta dace kuma ta zama ta ɗaya. Aisha Sani Abdullahi, da ita kuma aka fi saninta da Ɗayyeeshatul Humaira marubuciyar littafin ‘Sai Na Auri Marubuci’ sau uku ita ma tana ƙoƙarin shiga gasar Hikayata da fatan samun nasara. 

Malam Jibrin Adamu Jibrin Rano, shi ne jagoran zauren ‘Aji Na Musamman’ a manhajar WhatsApp inda akasari waɗannan marubuta suke samun bita da wayarwa akan dabarun rubutun littafi da gajerun labarai, a ganinsa, “Gasar Hikayata ta BBC Hausa ta zamewa marubuta mata kamar zuwa aikin Hajji, inda kowanne marubuci ke son zuwa don sauke farali. Babu marubuciyar da take so a bar ta a baya wajen shiga gasar Hikayata. Sai dai ba kowacce ba ce Allah Ya ke kira, sai mai tsananin rabo!”

A bana, a cewar mahukuntan tashar BBC Hausa, gasar Hikayata ta samu labarai har kimanin 500 da marubuta daban-daban suka shiga gasar da su, amma bayan nazari da tantancewa da alƙalan gasar suka yi an fitar da sunayen labarai 15 da suka yi rawar gani da fitar da jigo masu muhimmanci da alƙalan suka yabawa.

Kafin kuma daga bisani aka fitar da sunayen gwaraza 3 da Allah Ya bai wa nasarar zuwa mataki na ƙarshe. Waɗanda aka sanar da sunayensu a ranar 27 ga watan Nuwamba, 2023. Yayin da kuma duniya ta shaida yadda aka fitar da matsayin da kowanne ya samu a ranar 30 ga watan Nuwamba, 2023, inda kuma aka karramasu da kyautar kuɗaɗe masu yawa daga Hukumar Gudanarwar BBC Hausa da wasu fitattun mutane. 

Wacce ta zo ta farko Aisha Adam Hussaini da labarinta mai suna ‘Rina A Kaba’ ta samu kyautar Naira Miliyan ɗaya, sai wacce ta yi na biyu Aisha Abdullahi Yabo da labarinta mai suna ‘Baqin Kishi’ ta samu Naira dubu 750, yayin da Aisha Sani Abdullahi da labarinta ‘Tuwon qasa’ ya zo na uku ta samu Naira dubu 500. Wani abin arashi da burgewa shi ne dukkansu marubutan sunansu Aisha!

Malam Jibrin Adamu Jibrin Rano ya ƙara da cewa, “Abin alfahari ne kasancewar dukkan gwarazan wannan shekarar ɗaliban ‘Aji Na Musamman’ ne, kodayake tun daga shekarar 2021 kowacce shekara sai an samu ko da marubuciya ɗaya ne daga ajin da za ta zama gwarzuwar Hikayata. Tabbas abin daɗi ne matuƙa, abin farinciki da alfahari ne,domin dai hakan ya nuna tasirin haɗuwa inuwa ɗaya da ake yi, ana ƙara wa juna sani.” 

Daga cikin abubuwan burgewa da Gasar Hikayata ta BBC Hausa ta bambanta da sauran gasanni, sun haɗa da tsari da tsauraran dokokin da aka sanyawa gasar. Kamar yadda alƙalan gasar suka yi bayanin yadda ake tafiyar da tsarin alƙalancin, wanda shi ma kawai ya isa ya tabbatar da akwai adalci a ciki. Sannan zaɓar ƙwararru daga ɓangarori daban-daban yayin alƙalancin shi kansa alama ce da ke nuna akwai tsarin yin adalci da kawar da zarge-zarge a gasar. Ko ma a yadda BBC Hausa ta haramtawa ‘yan’uwan ma’aikatanta shiga gasar shi ma abin a yaba ne. 

Aisha Sani Abdullahi ta ce, bayan shiga gasar Hikayata har sau uku ba ta yi nasara ba, taso ta karaya ta daina shiga, amma kuma da taimakon Allah da ƙarfafa gwiwar da take samu wajen wasu daga cikin marubuta ya sa har ta kai ga cin wannan nasarar.

Ita kuwa Aisha Adam Hussaini, gwarzuwar shekara godiya ta yi wa mijinta Malam Aminu Kundila da ƙawarta marubuciya Maryam Muhammad Sani, wacce ta zama gwarzuwa ta 3 na gasar Hikayata na shekarar da ta gabata. Saboda yadda suka riƙa ƙarfafa mata gwiwa da taya ta duba labarin da ta samu nasara da shi ‘Rina A Kaba.’

A cewar Aisha Fulani ƴar mutanen Yabo, burinta na samun nasara da cigaba a harkar rubutu shi ne abin da ya fi ƙarfafa mata gwiwa ta cigaba da nacewa tana shiga gasar har tsawon shekaru 5, kafin wa’adin da ubangiji ya ƙaddara mata samun nasara ya yi. 

Misalin yadda Malam Jibrin Adamu Rano ya kwatanta gasar Hikayata da kiran ubangiji ne kamar aikin Hajji, ga Hajara Ahmad Maidoya da aka fi sani da Oum Nass, har yanzu nata lokacin bai zo ba, duk kuwa da kasancewar sau huɗu tana shiga gasar, kuma ta sha samun nasara a wasu gasanni daban-daban. Domin kuwa tana cikin gwarazan gasar Gusau Institute ta shekarar 2022, inda littafinta na ‘ɗanyen Kasko’ ya samu nasara a mataki na biyu. Amma a gasar Hikayata har yanzu ba ta samu damar shiga cikin fitattun marubuta ba!

Sai dai duk da haka Oum Nass ta ce, matuƙar tana raye ba za ta daina shiga gasar Hikayata ba, har sai lokacin da haqarta ta cimma ruwa. Kuma wannan ra’ayi nata ya zo daidai da na marubuciya Faridat Husain Mshelia marubuciyar littafin ‘First Ramadan With Habibi’, wacce ta ce sau uku ita ma tana shiga gasar Hikayata, sai a wannan shekarar ne labarinta mai suna ‘Tsalle ɗaya’ ya samu shiga sahun labarai 15 da suka nuna bajinta. Ta ce, wannan ma babbar nasara ce a gareta, domin shiga cikin wannan sahun yana nuna akwai alamun ƙamshin nasara a kusa. Don haka za ta cigaba da shiga gasar Hikayata, har Allah Ya datar da ita ta samu shiga cikin Gwaraza Ukun da ake karramawa a gasar. 

“Babban burina,” inji Faridat Mshelia. “Ina so in samu nasara ne saboda in yi amfani da wannan damar wajen ganin saƙona ya shiga kunnuwan miliyoyin mata da ke rayuwa a karkara da birane. Domin babban burina ƴaƴa mata su farka daga barcin da suke yi, su miƙe tsaye ƙyam su san rayuwa ta canza. Sam, kuɗin da ake bayarwa ba shi ne a raina ba.” 

Kodayake akasarin marubuta mata wannan shi ne ra’ayinsu na, su isar da saƙo ga mata ƴan’uwansu, don su fahimci rayuwa, amma ba don kuɗin da Hukumar BBC Hausa take bayarwa na tukwici ga marubutan da suka samu nasara a matakin ƙarshe ba. Sai dai duk da haka abin da ake bayarwa ɗin yana ƙarfafa musu gwiwa. A cewar gwarzuwa Aisha Adam Hussaini, “Gasar Hikayata ta taimaka wajen zama silar da mata marubuta da dama suka samu tarin nasarori da cigaban rayuwa.” 

Ta ƙara da cewa, “Ina da niyyar yin abubuwa da dama da kuɗin da na samu. Sai kuma babban burin da ke raina wanda ya kasance tsakanina da Ubangiji ne. Amma ina fatan wannan ya kasance jarin da zan kafa, wanda zan girbi ribarsa a ranar gobe ƙiyama.” 

Har kawo lokacin haɗa wannan rubutun, Aisha Abdullahi Yabo ba ta gama shawarar mai za ta yi da nata kuɗin da ta samu ba. A cewarta, “Amma ina dai fatan Allah Ya min ilhamar yin abin da zai amfane ni duniya da lahira.

“Babban burina bai zarce a ce na sanya farinciki a fuskokin al’umma ba. Tabbas zan yi ƙoƙarin yin duk wani abu da ya dace ga al’umma, domin nasarata ta zama silar alfaharinsu kuma bango abin jinginarsu.” Kamar yadda Aisha Sani Abdullahi ta bayyana nata ƙudirin kan abin da take shirin yi da wannan kuɗi da ta samu. 

Bincike ya nuna cewa, tuni dai waxannan gwaraza sun fara kasafta wani sashi na waɗannan kuɗaɗe da suka samu zuwa ga aljihun wasu daga cikin abokan rubutunsu maza da mata, malamansu da ke taimaka musu da shawarwari da gyare-gyaren ƙa’idojin rubutu, ƴan’uwa da iyaye. 

Muttaqa A. Hassan da aka fi sani da Yaya Muttaqa na daga cikin marubutan da suka samu nasu tukwicin daga alherin da waɗannan gwaraza suke yi ga wasu ƴan’uwa marubuta, inda ya bayyana farincikinsa da godiyarsa ga alherin da aka yi masa, a matsayin yabawa da gudunmawar da yake bayarwa a harkar cigaban rubutun adabi. Ya kuma shawarce su da su yi tattalin damar da suka samu wajen amfani da kuɗaɗen, don su ja jari, su qarfafa sana’o’insu, da harkokinsu na rubutu. 

Su ma a nasu ɓangaren, gwarazan Hikayata ta bana, sun ja hankalin sauran ƙawaye da abokan rubutunsu da suka daɗe suna shiga gasar amma Allah bai sa sun yi nasara ba, da su ƙara nuna haquri da jajircewa. A cewar Aisha Sani Abdullahi, “Su sa a ransu cewa za su iya, kuma su dage da addu’a, su yi aiki tuƙuru sannan su cire hassada da qyashi ga kowa a zuciyarsu. Tabbas matakin nasara tudu ne da ƙila a yi ta hawa ana faɗuwa, amma duk ranar da aka yi nasarar hayewa shi kenan kuma.”

“Ina son ‘yan’uwana marubuta mata su jajirce, su bazama lalubar jigon da ke damun al’umma, su yi rubutu a kai. Sannan su bai wa masana su duba musu, sai kuma su bi labaransu da addu’a. Domin addu’a ita ce ke kai mutum ga matakin nasara.” A ta bakin gwarzuwar shekara Aisha Adam. 

Ita ma Aisha Fulani cewa ta yi, “Duk abin da za su yi rubutu a kansa wajen shiga gasar su sa nazari sosai kafin ɗora alƙalaminsu. Haka kuma su ba masana su duba masu labarin su kafin turawa, kar kuma su sanya gaggawa wajen tura labarinsu. Sai kuma babban makamin samun nasara ita ce addu’a, su riƙi addu’a idan har da rabo, in sha Allahu sai a ga an dace.”

Malam Jibrin Rano shi ma irin wannan shawarar ya bai wa ɗaukacin marubuta mata masu burin shiga gasar Hikayata, inda yake cewa,” Kada su tava karaya har zuwa lokacin da za su kai matakin nasara. Ina yawan ba da misali da kaina a gasar Gusau Institute ta Kaduna, sau biyu ina shiga gasar labarina yana fitowa matakin kusa da ƙarshe, amma ina faɗuwa. Sai a na ukun ne na kai ga nasara a babban matakin. Da a ce na sare, ko kuma na munana zato wataƙila da ban zamo mai nasarar ba.”

Su ma mahukuntan tashar BBC Hausa an ba su shawarar su riƙa faɗaɗa yadda suke zaɓar alƙalan da ake bai wa aikin tantance labaran da ake shiga da su a gasar. Kada a riƙa tsayawa kan malaman Hausa da ke jami’o’i da manyan makarantun ilimi kawai, a maimakon haka a riqa sirkawa da marubuta da aka amince da ƙwarewarsu waɗanda za su taimaka wajen alƙalancin gasar.

Sannan su ma marubutan da labaransu ke kai wa matakin kusa da na qarshe, wato ajin labaru 15 da ake fitarwa na farko, wanda daga bisani ake ware fitattu uku a bar 12. Marubutan na roƙon su ma a riqa ware musu wani ɗan abin tukwici da za a basu, a maimakon takardar shaidar shiga gasar kawai da aka saba bayarwa a baya. 

Akwai kuma masu ba da shawarar a riƙa gayyato manyan baƙi da masu hannu da shuni daga maƙwaftakan ƙasashe irin su Jamhuriyar Nijar, Kamaru da Chadi, har ma da Ƙasar Ghana, inda ake da Hausawa da kuma masoya bunƙasa harkokin adabi da rubuce-rubuce. Domin su ma su zo su ba da tasu gudunmawar.

Gabakiɗaya dai gwarazan Hikayata na 2023 sun yi kyakkyawar jinjina da godiya mai yawa ga shugabanni da ɗaukacin ma’aikatan BBC Hausa da suka ce sun nuna musu halin karamci da mutuntawa, fiye da yadda suke tsammani. 

Allah Ya kai mu na baɗin baɗaɗa, da rai da lafiya.