Marubutan Arewa sun yi taron alhinin rasuwar Sheikh Yusuf Ali

DAGA MUKHTAR YAKUBU

An bayyana fitaccen malamin addinin Musluncin nan marigayi Sheikh Dakta Yusuf Ali wanda Allah ya yi wa rasuwa a farkon watan Nuwamban da ya gabata a matsayin wani managarcin malamin da ya yi shaharar da za a daɗe ba a manta da shi ba a fannin ilimi da kuma mu’amala da jama’a 
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin shugaban majalisar malamai ta Arewa da kuma ta Jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil a lokacin da yake gabatar da jawabin sa a wani taro da gamayyar ƙungiyar marubutan Arewa da ƙungiyar ANA ta ƙasa reshen Jihar Kano suka shirya domin tunawa da kuma nuna alhini ga rasuwar fitaccen malamin Sheikh Dakta Yusuf Ali.

Taron wanda aka gudanar da shi a ranar Lahadi, 3 ga Disamba, 2023 a ɗakin karatu na Murtala Muhammad da ke titin Ahmdadu Bello, a Kano, ya samu halarta Malamai, marubuta da kuma manazarta in da aka yi jawabai kan tarihi da kuma irin gudunmawar da shehun malamin ya bayar a fannoni da dama tsawon rayuwar sa.

Sheikh Ibrahim Khalil wanda shi ne jagoran zaman taron ya yi jawabi mai tsawo dangane da haƙuri da mu’amala da jama’a wanda marigayi Sheikh Yusuf Ali yake da su.

Sannan a cewar sa “Yusuf Ali a matsayin na mai basira, ya yi waqoqin da ya nuna fasahar sa wajen tsara baitoci cikin hikima da kuma bayyanar da ilimi da tarbiyya, don haka a ta kowanne vangare, idan muka duba za mu ga mun yi babban rashin malami. Don haka muna roqon Allah ya gafarta masa ya kuma kyautata bayansa.”

Shi ma da ya ke jawabi, babban baƙo mai jawabi a wajen, Farfesa Ibrahim Garba Satatima a wata takarda da ya gabatar a wajen mai taken, ‘ Sheikh Yufuf Ali Nagari na Kowa’ ya yi bita a kan tarihin rayuwar sa tun tasowar sa da kuma gwagwarmayar da ya sha har zuwa komawar sa ga Allah.

Daga cikin abubuwa na halayyar Sheikh Yusuf Ali da farfesan ya kawo har da haqurin sa da kuma nuna dattako a dukkan lamuran sa na rayuwa, kamar kyauta da kuɗi ga makwafta wanda kuma aikin da ya yi na ƙarshe a rayuwar sa shi ne, aikawa da kyaututtuka da ya sabar wa maƙwaftan sa.

“An yi wannan kyautuka da yamma kuma zuwa dare Allah ya karbi abin sa. Wani hali kuma shi ne, taimakon matasa. Domin tun bayan rasuwar malam Adamu na Ma’aji, ƙungiyar Fityanul Islam da yake jagoranta shi ne ya riƙe ta, kuma har Allah ya yi masa rasuwa matasa na ƙungiyar ba su tava samun matsala da shi ba, in dai sun je da buƙata zai shige musu gaba ya yi musu jagoranci a wajen kowanne mutum da suke son gani.

Baya ga haka, daga cikin halayyar sa, yana taimako ta hanyar malunta. Da an yi maganar malunta a Ƙasar Hausa, to Malam yana bada surruka da suke taimaka wa mutane daga cutukan da suke damun su na sarari da na ɓoye. Don haka wannan abu na malumta da Malam ya yi shuhura da su, sun sa ya yi fice wanda bayan shi ba a samu mai irin wannan ba, sai dai Malam Lawan Ƙalarawi.

Haka nan Malam idan an koma ɓangaren waƙa, nan ma ya yi fice don haka shi tunanin sa ya sha bamban da na sauran malamai,” inji shi.

Shi ma a nasa jawabin, Farfesa Bello Sa’id, ya bayyana Sheikh Yusuf Ali a matsayin mawaƙin da ya yi shaharar da babu kamar sa, domin duk wani fanni na rayuwa ya yi waƙa a kansa kamar fannin noma, kiwo, soyayya, aure, da kuma addini. Don haka Malam Yusuf Ali Gwarzo ne abin koyi.

Farfesa Aliya Adamu Ahmad daga Jami’ar Jihar Sokoto wadda ta yi ɗan gajeren jawabi ta onlayin. Ta yawa ba marigayi Yusuf Ali dangane da hikimar sa wajen tsara waqoqin da suka zama abin ajiyewa don tarihi, don haka a cewar ta, Sheikh Yusuf Ali ya bayar da gudunmawar da za a daɗe ana tunawa da shi.

Shi ma marubuci kuma ɗan jarida Malam Danjuma Katsina a jawabin da ya yi ta onlayin. 

Ya ce, “Lallai Sheikh Yusuf Ali ya bayar da gudunmawar sa sosai a fagen aikin jarida, domin shi ne malami na farko da ya rinƙa sayen shafuka a jaridu da kuma gidajen rediyo don gabatar da shirin sa na Ilimi Kogi ne, wanda hakan ba ƙaramin ci gaba ya samarwa kafafen yaɗa labarai da kuma aikin jarida ba.”

Jama’a da dama dai kamar su Ado Ahmad Gidan Dabino (MON), Aminu Ladan Alan Waƙa, Khalid Imam, da sauran su sun yi jawabai a kan shehun nalamain tare da alhinin rasuwar sa, kasancewar sa wani babban givi mai wuyar cikewa.

Da yake jawabin godiya, Sheikh Misbahu Yusuf Ali, wanda shi ne Khalifan Malam a yanzu. 

Ya nuna farin cikin sa ga Ƙungiyar Marubuta ta Arewa da kuma ta ANA bisa taron da suka shirya na tunawa ga mahaifin su, wanda kuma a cewar sa, hakan ya nuna malamin na kowa ne ba ‘ya’yansa da danginsa ba kaɗai.

“Don haka muna godiya da wannan karamcin da aka yi mana, mun gode Allah ya bar zumunci,” Inji Sheikh Misbahu Yusuf Ali.