Morocco ta karɓi jagorancin Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta MDD

Morocco ta yi nasarar lashe kujerar shugabancin Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta MDD bayan da ta doke abokiyar hamayyarta a wannan mukami wato Afirka ta Kudu.

Bayan da aka bayyana nahiyar Afirka a matsayin wadda za ta shugabancin hukumar a wannan shekara ta 2024, duk da haka kasashen biyu wato Afirka ta Kudu da Morocco sun gaza cimma jituwa a tsakaninsu sai da aka je ga kada kuri’a.

A quri’ar da aka kada a asirce ranar Laraba a birnin Geneva, dan takarar Kasar Morocco Omar Zniber ya samu kuri’u 30 yayin da abokin karawarsa Mxolisi Nkosi na Afirka ta Kudu ya samu kuri’u 17, sakamakon da ya yi matukar bai wa masu fafutuka a duniya mamaki.

Morocco wadda ke karkashin jagorancin gidan sarauta, ta na daga cikin kasashen da ake zargi da tauye hakokkin bil’adama da suka hada rashin shimfiduwar tsarin dimukuradiyya, yayin da a hannu daya ake zargin ta da cin zarafin al’ummar yankin Yammacin Sahara da ke neman ‘yancin kai.

Bayan kammala wannan zabe, wanda ya yi nasara Omar Zniber daga Morocco ya ce zai iya kokarin sa domin kara inganta ayyukan hukumar, yayin da wanda ya sha kaye Mxolisi Nkosi, ya bayyana mika kujerar ga Morocco a matsayin kaskanci da zai iya shafar kimar wannan hukuma da ke wakiltar Majalisar Dinkin Duniya a batutuwan da suka shafi kare hakkin dan adam.