’Yan ta’adda sun gama yawo, inji Hedikwatar Tsaro

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hedikwatar Tsaron Nijeriya a ranar Alhamis ta sha alwashin bin diddigin ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka a fadin kasar har sai an fatattake su ko kuma su mika wuya.

Rundunar ta tabbatar da cewa a makon farko na shekarar 2024 dakaru sun kai hare-hare ta sama da dama kan yankunan ‘yan ta’adda tare da yin amfani da karfin soji a dukkan yankunan da ‘yan ta’adda suka addaba a kasar.

Daraktan Yada Labarai Na Tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a Abuja, inda ya ce rundunar ta kara zage damtse wajen farautar ’yan ta’adda da sauran masu aikata miyagun laifuka a kasar.

Janar Buba ya ci gaba da ayyana dukkan ’yan ta’addan a matsayin ‘matattu masu tafiya’ tare da ba da tabbacin cewa sojoji za su cigaba da farautar su har sai sun kawar da su ko kuma sun miqa wuya ga sojoji.

“Ayyukanmu sun nuna cewa muna farautar kwamandojin ’yan ta’adda da manyan shugabanninsu. Lallai tun daga mafi girman shugabancinsu har zuwa mafi qarancin kwamandojin su matattu ne masu tafiya kuma ba za mu daina komai ba har sai sun mutu ko sun mika wuya.”

Dangane da aikin, Daraktan ya ce, a cikin wannan mako, sojoji sun kashe ’yan ta’adda 86 tare da kame ‘yan ta’adda 101, masu satar mai 30 tare da kubutar da mutane 21 da aka yi garkuwa da su.

Ya ce, a yankin Arewa maso Gabas, dakarun Operation HADIN KAI gabadaya, sun kashe ’yan ta’adda 20, sun kama 4 tare da kubutar da mutane 40 da aka yi garkuwa da su.

Yayin da suke yankin Arewa ta Tsakiya, duka sojojin Operation SAFE HAVEN da WHIRL STROKE sun kama wasu masu tsatsauran ra’ayi guda 21, tare da ceto mutane 27 da aka yi garkuwa da su a hare-haren da suka kai a yankin a cikin wannan lokaci.

Janar Buba ya bayyana cewa dakarun Operation WHIRL PUNCH da HADARIN DAJI sun samu gagarumar nasara a yankin Arewa maso Yamma yayin gudanar da ayyukansu.

“Bakidaya, dakarun Operation HADARIN DAJI sun kashe ‘yan ta’adda 56, sun kama 10 tare da kuvutar da mutane 40 da aka yi garkuwa da su.

Arewa maso Yamma; “Gabadaya, dakarun Operation WHIRL PUNCH sun kashe ’yan ta’adda 13, sun kama 15 tare da kubutar da mutane 23 da aka yi garkuwa da su,” inji shi.

Ya ce ayyukan da sojoji ke yi a yankin Neja Delta sun hana masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa lalata kadarorin kasa na Naira Miliyan Dari Bakwai da Sha Biyar da Dari da Dari da Saba’in.

Ya qara da cewa, sojojin a lokacin da suke kai hare-hare a fadin kasar, sun kwato tarin makamai daga hannun masu laifin.

“Sojoji sun kwato makamai iri-iri 111 da alburusai iri-iri 1,124. Bidigogin AK47 guda 65, HK G3 dun daya, bindigar G3 guda 8, bindigu na gida guda 8, bindigogin Danish 15, bindigu na kirkirar gida guda 2, bindigar gida guda daya, bindigar baushe daya, bindigar famfo guda daya, bindigar mota guda 2, bindigogin ganga guda.

Daraktan ya kuma shawarci daukacin ‘yan Nijeriya da kada su amince da ‘yan ta’adda da sauran miyagun ayyuka a kasar, inda ya yi kira ga kowa da kowa da su hada kai da sojoji da sauran jami’an tsaro domin yaqar rashin tsaro a fadin kasar.