Badaƙalar Ma’aikatar Jinƙai: Babu ’yan mowa a wajen Tinubu – Shugaban ICPC

Spread the love

*Yadda Hukumar EFCC ta ƙwace fasfon Sadiya, Edu da Halima

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sabon Shugaban Hukumar Yaki da Ayyukan Almundahana Mai Zaman Kanta (ICPC), Malam Musa Aliyu, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai ware wani ko wasu ya ce ‘yan mowansa ba ne ko shafaffu da mai.

Ya ce, duk wanda aka kama da laifin cin rashawa a gwamnati, duk girmansa kuma duk matsayinsa, to za a kama shi kuma a hukunta shi.

Aliyu, wanda babban lauya ne, wato SAN, ya yi wannan bayani a ranar Laraba, a yayin da ya ke ganawa da manema labarai a Abuja.

Ya na maganar ce a matsayin amsar wata tambaya da aka yi masa dangane da wasu ‘yan tsugudidin da ke hana ruwa gudu, masu kawo wa yaki da cin hanci da rashawa cikas.

Malam Aliyu, wanda ya fara aiki a matsayin Shugaban ICPC na biyar cikin Disambar 2023, ya yi alkawarin fafata yaki da rashawa iyakar qarfin ikonsa.

Yayin da aka tambaye shi ya zai yi idan Shugaban Kasa ya ce a daina bibiyar wani batun wuru-wuru ko rashawa, sai Aliyu ya ce, “ai abin da Shugaba Tinubu ya yi cikin kwanakin nan uku ya isa ya zama shaida game da irin yadda wannan gwamnati ta nuna cewa ba da wasa take ba a batun yaki da cin hanci da rashawa.”

Maganar na da nasaba dangane da yadda Tinubu ya dakatar da Ministar Harkokin Agaji da Jinkai, Betta Edu, bisa zargin walle-walle da miliyoyin kudaden hakkin tallafin marasa galihu.

Shugaban na ICPC ya yi alkawarin cewa shi da kan sa zai rika tsayawa a gaban kotu, a matsayinsa na babban lauya ya na gurfanar da masu laifi, kuma ya bi shari’ar har zuwa lokacin yanke hukunci.

Bayan gayyayar da Hukumar Yaki da Ta’annatin Kudi da Tattalin Arziki (EFCC) ta yi wa tsohuwar ministar Buhari a ma’aikatar Jinkai da Agaji, Sadiya umar Farouq da dakatacciyar Ministar Jinkai ta yanzu, Betta Edu, a cikin makon nan, hukumar ta kuma kwace fasfo dinsu kan binciken badakalar da ake yi a ma’aikatar.

Wata majiya mai tushe daga hukumar ta EFCC ta ce, an kwace fasfo din Edu da Sadiya ne, domin hana su fita daga Nijeriya yayin da ake cigaba da binciken.

Hukumar, wacce ta kwace fasfo din tsofaffin ministocin biyu, Sadiya Umar-Farouq da Betta Edu, majiyarmu ta kuma ce, “mun kuma kwace fasfo din Halima Shehu har sai an kammala bincike. Hukumar ba ta son yin kasadar ganin ko daya daga cikinsu ya fice daga Nijeriya alhalin ana bincike a kan su.”

Dangane da binciken Edu da Sadiya Umar-Farouq, EFCC ta gayyaci shugabannin bankunan Zenith, Providus da Jaiz ofishinta a ranar Talata.

Ita ma Halima Shehu, wacce aka dakatar daga hukumar kula da harkokin zuba jari ta kasa, EFCC na bincike a kan ta.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, Edu ta isa hedikwatar EFCC da misalin karfe 10 na safiyar ranar Talata domin amsa tambayoyi kan zargin almundahanar kudi da ake mata.

Wannan na zuwa ne bayan fitar wata takarda da ta nuna cewa Edu ta bukaci babban Akanta-Janar na Tarayya ya biya Naira miliyan 585 da aka ware wa marasa galihu zuwa wani asusun banki na daban.

Bayan matsin lamba da ’yan Nijeriya suka yi, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan Edu da kuma ayyukan ma’aikatar.

A nata bangaren kuma, Sadiya Umar-Farouq, tsohuwar minista a lokacin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ita ma EFCC ta gayyace ta domin amsa tambayoyi kan zargin da ake mata na sama da fadi da sama da biliyan 37.

By Editor