Daga BASHIR ISAH
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris Malagi mamba a kwamitin bincike da zai binciki shirye-shiryen yaki da talauci karkashin hukumar NSIPA.
Kafa kwamitin binciken da Tinubu ya yi ya biyo bayan dakatar da shirye-shiryen yaki da talauci guda hudun da ke karkashin NSIPA da ya yi ne na tsawon wata shida bisa zargin aikata ba daidai ba a hukumar.
Kwamitin zai gudana ne karkashin jagorancin Minista mai kula da Tattatilin Arziki kuma Ministan Kudi, Mr. Wale Edun, in ji sanarwar da Kakakin Shugaban Kasa, Cif Ajuri Ngelale ya fitar ran Asabar.
Ta kara da cewa, an dora wa Kwamitin nauyin bincike kan ka’idoji da kuma yadda ake gudanar da harkokin shirye-shiryen yaki da talauci da zummar samar da canje-canjen bunkasa su yadda ya kamata.
A cewar sanarwar, Kwamitin Shugaban Kasa kan binciken ya kunshi ministotcin muhimman bangarorin gwamnati da suka hada da Ministan kula da tattalin arziki kuma Ministan Kudi, Wale Edun, a matsayin shugaba; Ministan Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris; Ministan Lafiya da Kyautata Rayuwa, Farfesa Ali Pate da kuma Ministan Kasafi da Tsara Tattalin Arziki, Atiku Bagudu.
