Mutanen Gaza ba su gaza ba bayan kashe dubbai

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Fiye da mako 6 kenan sojojin Isra’ila su na ruwan wuta kan Gaza inda Falasɗinawa fiye da miliyan 2 da ke zaune a garin musamman arewacin sa ke zama cikin yiwuwar afkuwar komai a kullum. In za a tuna Isra’ila ta buƙaci Falasɗinawan su kaura zuiwa kudancin Gaza don kare ran su daga boma-bomai. Duk da dai ba lalle ba ne can kuɗin ma tudun mun tsira ne amma ya fi yankin arewaci ‘yar sararawar hare-hare, hakan bai sa dubban Falasɗinawa kauracewa gidajen su ba.

Wannan akwai abun dubawa a nan don ga gidajen an rushe su, ga ma wasu gine-ginen da a ka ruguza da bom sun danne su an kasa ceto su. wasu sun mutu ba a samu damar yi mu su jana’iza ba. Da kuwa Falasɗinawa na jin tsoro da ba za a samu wani mai numfashi ya na rayuwa a yankin Gaza ta arewa ba. Sashen Falasɗinawan na fakewa a asibitoci wasu kuma na sansanin ‘yan gudun hijira na Jabaliya. Wa ma ya ke samun abinci bare ya ci ya ƙoshi. Ina ruwan sha ina magani a asibiti?

Mutuwar nan ba yara ba manya ba mata ba maza ba tsoffi; kowa kawai ajali ya zo shikenan ya tafi. Ina ganin wannan ya sa a ka yi hikiyar wani babban shugaban yammacin turai ya tambayi wani yaro Bafalastine cewa in ya girma me ya ke son zama? Yaro ya ce ai su ba sa girma bare su yi wani burin zama wani abu, ma’ana su a kan hallaka su tun su na yara ƙanana. Yaƙin nan ya tabbatar da wannan magana don adadin yaran da su ka mutu sun haura 5000.

Wanda ya tashi a Gaza ko ma garuruwan Falasɗinawa zai fi akasarin jama’ar wasu ƙasashe sanin tashin hankali ko mutuwar wanda mutum ya fi so kuma ba tare da akwai wani shirin ba da fansa ba. Duniya kamar ta kaucewa marmarin adalci ga Falasɗinawa. Ƙaddara ma ba ‘yan Hamas a cikin Falasɗinawa, wannan ba wai ya nuna za su zauna lafiya cikin ‘yanci ba ne, a’a za su cigaba da kasancewa sai yanda Isra’ila ta yi da su wato sai yanda Isra’ila ta dama haka za a sha ko ba a so. Ko a yanzu iya abun da Larabawa kan ce a kaucewa hallaka fararen hula.

To ai ba ma za mu ga laifin su ba ga wanda ya fahimci siyasar duniya. Duk da haka a ƙungiyance ƙasashen Larabawa na iya matsa lamba ga ƙasashen yamma su amince a ƙafa ƙasar Falasɗinawa mai ‘yanci. Har kullum manyan ƙasashen yammacin duniya na mara baya ne kai tsaye ga Isra’ila. Duk ƙasar Larabawan da ta nemi taimakawa Falasɗinawa fiye da fatar baki da tallafin kuɗi ko abinci, to za ta shiga bakin littafi. Wato inda ƙasashen na Larabawa na da shugabanni da ba masu son dauwama kan mulki ba to da za su iya taɓuka abun kirki wajen kare Falasɗinawa.

Hare-hare biyu da Isra’ila ta kai kan sansanin gudun hijira a arewacin Gaza ya yi sanadiyyar mutuwar Falasɗinawa 80.

Sansanin na Jabaliya shi ne mafi girma a yankin kuma a lokacin harin ya na ɗauke da jama’ar da su ka rasa muhallan su a sanadiyyar ruguje mu su gidaje da Isra’ila ta yi.

Harin ya shafi hatta wata makaranta ta Majalisar Ɗinkin Duniya kuma an ga hotunan gawawwaki a zube a ƙasa cikin jini.

Jami’an jinkai na Majalisar Ɗinkin Duniya na kiran dakatar da buɗe wuta a yankin Gaza a matsayin hanya ta kawo ƙarshen mugun yanayi da jama’ar yankin ke ciki.

Ɗaya daga jami’an Volker Turk ya ce aƙalla ɗaya daga Falasɗinawa 57 da ke zaune a Gaza wa imma an kashe shi ko an raunata shi.

Turk ya ce yanayin na da matuƙar munin gaske fiye da kenan yadda a ke tunani.

A nan an buƙaci Isra’ila ta daina amfani da datse ruwan sha a matsayin hanyar karya lagon ‘yan Hamas don hakan na shafar jama’a ne ciki da majinyata da su ka haɗa da jarirai da ke asibiti.

Hukumar kula da wadatar abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce mutum miliyan 2.2 da ke Gaza na cikin gararin afkawa yunwa.

Wannan na zuwa ne yayin da yanke makamashin fetur, ruwan sha da kayan abinci ke ta’azzara ga a’ummar ta Gaza da ke cikin farmakin da sojojin Isra’ila ke ƙara takarkarewa kan garin na su.

Jmai’ar labarun yanki ta hukumar abincin Abeer Etefa ta ce idan Falasɗinawa a Gaza su ka samu abinci sau ɗaya a wuni to wannan gagarumar nasara ce.

Kazalika mutane na dogara kan abincin gwangwani da a ke samarwa wanda kuma ko kusa baya wadatar da jama’ar da ke yanayin yaqi ga shi kuma an ruguza gidajen su.

Wata babbar damuwa ita ce rashin makamashi zai ƙara yi wa jama’a illa yayin da a ke fuskantar shiga yanayin hunturu.

Ƙungiyar ‘yan tawayen houthi a Yaman da Iran ke marawa baya ta yi barazanar kai hare-hare kan jiragen ruwan Isra’ila don martani kan yadda gwamnatin ta Yahudawa ke kai miyagun hare-haren kan Gaza.

Shugaban houthi Abdulmalik Al-houthi ya ce za su cigaba da farautar jiragen ruwan Isra’ila a Bahar Maliya da mashigar ruwan Babab Mandeb.

Houthi na daga ƙungiyoyin Larabawa da ke nuna fushi kan nuna ƙarfi fiye da kima da Isra’ila ke yi kan Falasɗinawa. Barazanar ta Houthi da kuma qungiyar Hezbollah ta ’yan Shi’a a Lebanon bai fi a ce motsi ya fi laɓewa ba ne don ba wani babban tasiri da zai yi kan Isra’ila da ke da mara bayan manyan ƙasashen duniya masu juya lamura bisa ga muradun su.

Yarima Muhammad bin Salman na Saudiyya ya gana da shugaban Iran Ebrahim Raisi a Riyadh inda su ka tattauna kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa kan Gaza.

Ganawar na gefen taron ƙungiyar Larabawa da ta ƙasashe musulmi kan fitinar da ta afkawa yankin Falasɗinawa.

Muhammad bin Salman ya buqaci sauran shugabanni da su maida martani na bai ɗaya, ya na mai Allah wadai da hare-haren da ya zayyana na jahilci da Isra’ila ke kai wa kan fararen hula a Gaza inda mata da ƙananan yara ke asarar ran su.

Yarima bin Salman ya buƙaci dakatar da zubar da jinin da a ke yi ga al’ummar Falasɗinawa da ya zaiyana su da ‘yan uwa.

Saudiyya ta jagoranci wani shirin kai tallafin kayan abinci da magani Gaza inda hakan kan yiwu kawai ta mashigar Rafah daga ƙasar Masar. Ita kan ta Masar ba ta sha’awar buɗe mashigar don kar Falasɗinawa ke shigo ma ta kasa kuma hakan zai saɓawa muradun kawayen Masar da ke mara baya ga Isra’ila.

A kwanakin baya Masar ta buɗe mashigar inda wasu majinyata na kure taya su ka samu damar ƙetarawa don samun magani. An ga hoton manyan motoci ɗauke da kayan masarufi da su ka shiga Gaza da wasu ma motocin da ke ɗauke da kayan makamashi amma duk ba zai kai mafi qarancin miƙadarin buqƙatun Falasɗinawan ba sai da da babu gara ba daɗi.

Sojojin Isra’ila sun zagaye wani babban asibitin arewacin zirin Gaza bayan mamaye asibirin Al-Shifa da ke tsakiyar yankin.

Hukumar lafiya ta duniya ta samu nasarar ɗauke ‘yan jarirai 31 da ke asibitin da Isra’ila ta fara kai wa hari wato Al-Shifa da ke cikin matuƙar hatsari daga yanayin lafiyar su.

Asibitin na Indunisiya na ɗauke da da mutane da daman gaske ciki da marar sa lafiya da kuma jama’ar gari da su ke fake a nan don tsira da ran su daga ruwan boma-bomai da Isra’ila ke yi.

Isra’ila na zargin cewa ‘yan Hamas na amfani da asibitocin don zama garkuwa gare su a fafatawar da su ke yi da sojojin na Yahudawa.

Gwamnatin Isra’ila ta sanar da cewa ta cimma yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta kan Gaza da ‘yan Hamas don amincewa da sako Yahudawa 50 cikin 240 da Hamas xin ta kama.

Firaministan Isra’ila Benjmain Netanyahu ya bayyana hakan bayan majalisar Yahudawan ta amince da tsagaita wutar na tsawon wuni 4.

Hakanan Netanyahu ya ce Isra’ila za ta riqa ƙara kwana daya a duk lokacin da Hamas ta sako Yahudawa 10.

Netanyahu duk da hakan ya ce da zarar an kammala sako fursunonin ko waɗanda Hamas ta kama, sojojin Isra’ila za su dawo da ruwan wuta kan Gaza.

Tsagaita buɗe wutar zai taimaka ne wajen shigar da kayan agaji Gaza ga mutanen da ke matukar son abinci, ruwan sha, magani da sauarn su.

Ko a yanzu Isra’ila ta kashe dubban Falasɗinawa a Gaza ciki kuwa akwai mata da ƙananan yara.

Kammalawa;

A yanzu da alqaluman Falasɗinawa da Isra’ila ta hallaka a Gaza su ka doshi 13000, baa bun da ya kamata a riƙa yi sai kiran kawo ƙarshen wannan yaƙi da kusan ba a taɓa samun mafi asarar rayuka irin sa ba a tarihin arangamar sojojin Isra’ila da ’yan Hamas. Hatta wannan tsagaita buɗe wuta na wucin gaɗi ne don karvo Yahudawan da Hamas ta yi garkuwa da su kuma ga shi Benjamin Netanyahu ya ce da zarar an gama karɓo Yahudawan za a cigaba da buɗe wuta.

In da ƙasashen Larabawa za su yi amfani da wannan dama wajen matsawa Amurka lamba ta tsawatawa Isra’ila ta dakatar da wannan yaƙi a wannan dan tsakani da ya fi a’ala. Adalci ne kan kawo salama a duniya kuma rashin sa kan sa ko an raina kama za a ga gayya.