Zuwa ga al’ummar Arewa

Spread the love

Assalamu alaikum. Bayan gaisuwa mai tarin yawa tare da fatan alheri gare ku duka, ina kuma mai jajanta muka akan halin da muka tsincin kanmu a yau.

Ina fatan wannan wasiƙar tawa ta same ku lafiya, cikin ƙoshin lafiya da walwala.

Na rubutu wannan wasiƙar ne domin na isar muku da saƙona tare da fatana gare ku. Ina mai shaida muku cewa, ƙaunarku ce ta sa na rubutu wannan wasiƙar, domin masu iya magana kan ce ‘Idan kunne ya ji…’ Wannan wasiqar ita ce babbar gudunmawar da zan iya bayarwa a halin yanzu, bayan koyar da yara da nake a makaranta.

Duk wata gudunmawa da zan bayar, ba ta kaita ba, don koyarwa ta fi ko wace irin gudunmawa. Domin kalamun da ke cikinta za su fi mana amfani a irin halin da muka tsincin kanmu A yau.

Kamar yadda muka sani a yau cewa, duk wasu jihohin Arewa babu kwanciyar hankali, jihohin Borno da Katsina da Zamfara da Kaduna da Taraba da Yobe sun zama tamkar sansanin ‘yan ta’adda, kullum a cikin zullumi da kisan kiyashi ake yi wa al’umma kai kace babu gwamnati a ƙasar.

Abu mafi muhimmanci da ya kamata mu mai da hankali a kai shi ne, neman ilimin addini da na boko. Amma fa mu sani, karatun addini shi ne ya zamo mai gudanar da rayuwarmu, ba na boko ba.

Da yawan ‘yan boko A yau sun watsar da addini sun bi kafirai sun kafirce wa Allah da Annabinsa, sun bijire musu, sun yi watsi da umarninsu, shi ya sa ma ake haɗa baki da wasunsu ake zaluntar mu.

Neman ilimi abu ne mai muhimmanci, domin babu wata ƙasa da ta ci gaba a duniya alhali tana yi wa ilimi riƙon sakainar kashi. Dole mu farga! Mu dawo cikin hayyacinsu, mu dawo daga rakiyar mutanen da basa qaunarmu, basa son ci gabanmu.

Mu zama musu dogaro da kai, ta hanyar ƙirƙirowa kanmu hanyoyin samun mafita na rayuwa. Wannan zai taimaka wajen fitar da Arewa daga halin da take ciki a yau. Babu wani dalili da zai sa mu zauna muna kiran babu aikin yi, alhalin Allah ya yi mana baiwa da hikimar dogaro da kai.

Matasanmu a yau ba sa son motsa jiki, kowa sai jiran ganima daga gwamnati, wanda wannan kuma babban kuskure ne. Allah bai ce kowane ɗan boko sai ya zama ma’aikacin gwamnati ba, kuma bai ce kowane ma’aikacin gwamnati sai ya zama mai kuɗi ba. Amma idan muka tsaya da ƙafarmu muka jajirce, Allah zai bamu mafita.

Kar mu ɗauka da zarar sun kammala karatun boko mun gama samun komai na rayuwar duniya. Lallai karatun boko abu ne mai kyau, domin zai haska mana hanyar da ya kamata mu bi ta fuskar ilimi, amma ba abin dogaro ba ne wajen neman duniya da rufin asiri, domin akwai waɗanda Allah ya yi wa arziki a yau, amma ko ajin firamare ba su tava shiga ba.

Zancen mutum ya zauna yana tunanin aikin gwamnati wannan ya kau, ya kamata mu zamo masu ƙwazo da himma wajen dogaro da kai, domin mafi yawancin abin da ke cutar da mu a yau ke nan, ragganci da sun ci a kwance, don mun ga wani ya ɗaukaka sai suce tilas sai mun zama tamkar shi, wanda idan aka yi rashin sa’a, sai mutum ya tsinci kansa a wani mugun yanayi wanda kan jefa al’umma cikin fargaba da tashin hankali.

Wannan ne kaɗai hanyoyin da ya kamata mu bi wajen kau da dukkan ‘yan ta’adda da ta’addanci a Arewa, saboda an rabamu da Ubangiji, kuma ana amfani da ‘ya’yanmu wajen rusa mu.

Da wannan na kawo ƙarshen wannan wasiƙar tawa. Ina roƙon Ubangiji Allah ya yi mana jagora, ya taimake mu a dukkan lamuranmu, kuma ya sa Arewa ta ci gaba da zama lafiya.

Ban san meye matsalar mu ba mu mutanen Arewa da a kullum idan ana magana kan raba Nijeriya tsakanin Kudanci da Arewacinta, sai ka ji muna cewa, “Ku bar su a rabu, ai idan an rabu (kudanci) za su sha wahala, saboda Yarabawa da Ibo basa ga maciji da juna, rikici ne zai kaure a tsakaninsu kamar yadda ya faru a Sudan ta kudu bayan ta fice daga Sudan.”

Mai yiwuwa wannan hasashe ya iya zama gaskiya, to amma ita Arewar fa? Wai a tunanin mu Arewar na iya zama a turbar son juna, qaunar juna, ’yan-uwantaka, dattaku da sanin yakamata a irin halin na-ciki-na-cikin da muke rayuwa, inda ake kallon-kallo ga juna?

Duk da yake cewa munfi ’yan kudanci rashin nuna bambance-bamcance a tsakanin juna, amma yana da kyau mu duba wasu vangarorin domin gyara, musamman batun da ya jibanci siyasa.

Misali mu duba cece-kuce da taɓargszar da take faruwa kwana biyun-nan tsakanin ’yan Arewan. A kullum z aka ga ɗan Arewa bai ƙaunar ci gaban ɗan uwansa, to shin a haka za mu cigaba da tafiya da sunan haɗin kai? Hatta a tsakaninmu muna hasada ga juna a kan matsayin da bai taka kara ya karya ba?

Ka da mu yadda wannan abu ya ci gaba da faruwa idan ba so muke a kasa bambancemu da waɗanda muke cewa kansu a rabe yake ba. Misali na biyu da zan baku shi ne, lokacin da ake rikicin Shugabancin jam’iyar PDP tsakanin Ali Modu Sherrif da Ahmed Makarfi, a bayyana.

Take cewa kowa na samun goyon baya ne na mafi akasarin mutane da gwamnonin da ke yankinsa a fahimta ta.

Inda ’yan yammacin Arewa ke rufa wa Makarfi baya, yayin da a vangarensu ’yan gabashin Arewa ke cewa Sheriff ba ja da baya. Shin wannan shi ne haɗin kan Arewar? Wallahi ya zama wajibi mu kyautata ’yan-uwanta ka a tsakaninmu domin tsira daga barazanar rabuwar kai da ’yan-uwantaka gami da dogon zumuncin al’adda da addinin da ke tsakaninmu, mu yi siyasa ta cigaba mai tsafta a garemu.

Wassalam. Daga Muhammad Auwal Musa (Ya Muha). 08062327373.

By Editor