Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 17,000 a cikin kwana 62

Daga BASHIR ISAH

Falasɗin ta bayyana cewa, Isra’ila ta kashe sama da mutum 17,000 a Gaza a cikin kwana 62 a ci gaba da gwabza yaƙi a tsakanin ƙasashen biyu.

Falasɗin ta ce daga cikin wannan adadi, 7,224 ƙanan yara ne, sai kuma mata 5,818, tsofoffi 478, jami’an kiwon lafiya 281, ‘yan jarida 77, sai kuma mutum 46,000 da suka jikkata.

Ta ƙara da cewa, a bayyana ne cewa galibin waɗanda faɗan ya fi shafuwa mata da ƙananan yara ne.

Waɗannan bayanai na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai da ƙasar Falasɗin ta fitar mai ɗauke da kwanan wata 11 ga Disamban 2023, wanda ta aike wa Tarayyar Nijeriya da kwafi.

Sanarwar ta ce idan ba a kira abin da ke faruwa a Gaza da kisan kiyashi ba, to ya kamata a samar wa yanayin ma’anar da ta dace.

Sanarwar ta ci taƙara da cewa, gidaje 43,000 ne aka lalata su baki ɗaya, sannan wasu 255,000 sun lalace sama-sama.

Ta ce, kimanin mutum miliyan 1.9 kwatankwacin kashi 80 na adadin al’ummar Gaza rikicin ya ɗaiɗaita, ya raba su da muhallinsu.

A cewar sanarwar, tun daga ranar 7 ga Oktoba, sojojin Isra’ila sun kashe kimanin Falasɗinawa 243 ciki har da ƙananan yara 65 a yammacin Gaza.