Kasashen Waje

Shakira ta amince da biyan Ƙasar Sifaniya tarar fam miliyan 6.5

Shakira ta amince da biyan Ƙasar Sifaniya tarar fam miliyan 6.5

Daga AISHA ASAS  Daga ƙarshe dai fitacciyar mawakiyar Colombia, Shakira ta cimma yarjejeniya da masu shigar da ƙara na Ƙasar Sifaniya kan sasantawa dangane da tuhumar almundahanar biyan haraji da ke kanta. Yarjejeniyar na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin fara zaman kotu da ita. Mawakiyar ta biya tarar Yuro miliyan 7.5m, duk da cewa, a buƙatar masu gabatar da ƙara a yanzu sun so a ɗaure ta tsawon shekara takwas, sannan a ci ta tarar Yuro miliyan 23.8, idan aka same ta da laifi.  Kamar yadda Blueprint Manhaja ta ruwaito maku a 'yan watannin baya, mawaƙiyar ta…
Read More
An sallami wata jaruma daga fim bisa wallafa goyon bayan Falasɗinawa

An sallami wata jaruma daga fim bisa wallafa goyon bayan Falasɗinawa

Daga AISHA ASAS  Wata jaruma da ta ke aikin ɗaukar wani fim mai suna 'Scream' ta zama korarriya dalilin wallafa saƙon nuna goyon bayanta ga Ƙasar Falasɗinu, tare da barranta kanta daga irin kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza. Jarumar ta nuna matuƙar damuwa da halin da mutane ke ciki a Gaza, inda akai-akai ta ke wallafawa a shafukanta na sada zumunta ababen da ke wakana dangane da yaƙin Isra'ila a Gaza. A cikin irin rubutun nata, jarumar mai suna Melissa Barrera, ta zargi Isra’ila da aikata 'kisan ƙare dangi' wanda ke da ƙudurin shafe wata al'umma daga…
Read More
Hare-haren Isra’ila kan Falasɗinawa: Ban taɓa ganin irin wannan rashin imani ba – Abu Shawesh

Hare-haren Isra’ila kan Falasɗinawa: Ban taɓa ganin irin wannan rashin imani ba – Abu Shawesh

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jakadan Falasɗinawa a Nijeriya, Abu Shawesh ya bayyana cewa, bai tava ganin irin wannan rashin tausayi da tsantsan rashin ba kamar yadda Isra'ila ke ta varin wuta kan fararen hula a Ƙasar Falastɗinu. Ya ce, Martin Griffiths, a cikin hirarsa ta tashar CNN, ya ce, "bai tava ganin wani abu makamancin haka a baya ba, kisan gilla na rashin imani tsantsa." Ya ƙara da cewa, sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama, da harbin bindiga, harbin sari-ka-noƙe, har zuwa saukar da bama-bamai ta sama, adadin waɗanda suka mutu a tsakanin Falasɗinawa ya zarce dubu goma…
Read More
Isra’ila Ta Jefa Bam Mai Nauyin Ton 2500 A Gaza – Jakadan Falasɗinu

Isra’ila Ta Jefa Bam Mai Nauyin Ton 2500 A Gaza – Jakadan Falasɗinu

Daga WAKILINMU Jakadan ƙasar Falasɗinu a Nijeriya, Abdullah Abu Shawesh, ya ce mamayar da ƙasar Isra’ila ta yi a Gaza ba komai bane illa ta yi shi da nufin aiwatra da kisan kiyashi. Shawesh ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya kira a ofishin jakadancin ƙasar na Nijeriya dake Abuja. Kazalika ya koka kan yadda ake kai hare-haren kan fararen hula babu ƙaƙƙautawa waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, da sunan ana yaƙar dakarun Hamas wanda duniya ta san ba haka ba ne. da yake buga misali kan irin rashin imanin da Isra’ila…
Read More
Isra’ila ta amince da tsagaita wuta na sa’o’i huɗu a kowace rana a Gaza

Isra’ila ta amince da tsagaita wuta na sa’o’i huɗu a kowace rana a Gaza

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Fadar Shugaban Amurka ta White House ta ce Isra'ila ta amince da tsagaita wuta na tsawon sa'o'i huɗu a kowace rana a hare-haren da ta ke kai wa Hamas a arewacin Gaza daga ranar Alhamis, kamar yadda gwamnatin Biden ta ce ta samar da wata hanya ga fararen hula ta ficewa daga Gaza. Shugaban Amurka Joe Biden ya buƙaci Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ya kafa tsagaita buɗe wuta yayin kiran ranar Litinin. Kakakin Kwamitin Tsaron Amurka John Kirby ya ce za a sanar da tsagaita buɗe wuta na farko a ranar Alhamis, kuma Isra'ilawa sun…
Read More
Nijar ta nemi Togo ta shiga tsakani a rikicinsu da ECOWAS

Nijar ta nemi Togo ta shiga tsakani a rikicinsu da ECOWAS

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin sojan Nijar ta nemi Shugaban Ƙasar Togo, Faure Gnassingbe ya shiga tsakani a tattaunawa da ƙasashen duniya musamman ma Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Afrika ta Yamma (ECOWAS) wadda ta ƙaƙaba wa Nijar takunkumi tun bayan juyin mulki. Ministan tsaron Nijar, Janar Salifou Mody ne ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da Shugaba Gnassingbe a Lome babban birnin ƙasar ranar Litinin. Ya kuma nemi Togo ta tsayawa Nijar a yarjejeniyar janye sojojin Faransa daga ƙasar ta yankin Sahel. "Yana da muhimmanci a koyaushe mu tunatar da abokan kawancenmu cewa, ƙofar Nijar a buɗe…
Read More
Yunƙurin juyin mulki: Ana musayar wuta a ƙasar Guinea

Yunƙurin juyin mulki: Ana musayar wuta a ƙasar Guinea

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga ƙasar Guinea na nuni da cewa, ana zargin yunƙurin juyin mulki a ƙasar bayan da aka jiyo ƙazamar musayar wuta a Conakry, babban birnin ƙasar, a wannan Asabar ɗin. Shaidu sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, jami'an tsaro sun yi wa yankin ƙawanya, ba shiga ba fita. Wata majiya da aka sakaya sunanta ta ce, “Ana musayar wuta daga tsakanin ɓangarorin da lamarin ya shafa tare da harba makaman yaƙi a Kaloum." “Tun da asuba aka kulle garin, ba shiga, ba fita," in ji wani ɗan kasuwa a yankin. Guinea na ɗaya…
Read More
Nijar: An bankaɗo sabbin bayanai kan zargin Bazoum da yunƙurin tserewa

Nijar: An bankaɗo sabbin bayanai kan zargin Bazoum da yunƙurin tserewa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumomin shari’ar jamhuriyar Nijar sun sanar cewa binciken da suka gudanar ya bada damar gano wasu ƙarin bayanan da ke gaskanta zargin yunƙurin tserewar Shugaba Mohamed Bazoum da iyalinsa. Sun ce sun kama kuɗaɗe da dama da wasu tarin kayayyaki a fadar ta hamɓararren shugaban. Yayin da ya ke yin bayani a gidan talabijin ɗin RTN mallakar gwamnatin Nijar, mai shigar da ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara ta birnin Yamai, Salissou Chaibou, ya ayyana cewa bayanan da suka tattara sun gano cewa an ɗauki hotunan barikin dogarawan fadar shugaban ƙasa da suke zargin hamɓararren shugaban…
Read More
Tun 7 ga wata rayuka na cigaba da salwanta a Gaza

Tun 7 ga wata rayuka na cigaba da salwanta a Gaza

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Ba wani babban labari a duniya yanzu da ya sha gaban halin da a ke ciki a yankin Gaza na Falastinawa inda jiragen yaƙin Isra’ila ke cigaba da ruwan boma-bomai kan gine-gine da nuna zummar murƙushe ’yan bindigar HAMAS. Tabbas duk yadda za a iya auna masu rike da bindiga to la shakka sai an tava waɗanda ba ko allura a hannun su. Wani abun damuwa ma shi ne taba ran mata da yara. Bincike ma na nuna hatta jarirai ma ba su tsira ba. Kuma a gaskiya ba a san ranar da yaƙin ko…
Read More
Irin ta’asar da Yahudawa ke yi mana a Palastinu – Jakada Shawesh

Irin ta’asar da Yahudawa ke yi mana a Palastinu – Jakada Shawesh

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Jakadan Ƙasar Palastinu a Nijeriya, Abdullah Shawesh, ya bayyana irin ta’asar da ya ce Ƙasar Isra’ila (wato Yahudawa) suke yi wa al’ummar Palastinu na kisan gilla da kisan kiyashi kan waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, kamar ƙananan yara da mata, inda kawo yanzu aka kashe kimanin Palastinawa fiye da mutum 6,000, waɗanda fiye sa rabinsu yara ne ƙanana. Shawesh ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai, ciki har da Blueprint Mahhaja, a ofishin jakadancin Palastinu da ke Abuja ranar Laraba. Idan za a iya tunawa, a ranar 7…
Read More