Irin ta’asar da Yahudawa ke yi mana a Palastinu – Jakada Shawesh

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Jakadan Ƙasar Palastinu a Nijeriya, Abdullah Shawesh, ya bayyana irin ta’asar da ya ce Ƙasar Isra’ila (wato Yahudawa) suke yi wa al’ummar Palastinu na kisan gilla da kisan kiyashi kan waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, kamar ƙananan yara da mata, inda kawo yanzu aka kashe kimanin Palastinawa fiye da mutum 6,000, waɗanda fiye sa rabinsu yara ne ƙanana.

Shawesh ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai, ciki har da Blueprint Mahhaja, a ofishin jakadancin Palastinu da ke Abuja ranar Laraba.

Idan za a iya tunawa, a ranar 7 ga Oktoba, 2023, Ƙasar Isra’ila ta ƙaddamar da kai hare-haren da ta kira da ɗaukar fansa akan yankin Gaza a Ƙasar Palastinu, inda ake ta faman rasa rayuka da asarar dukiyoyi, lamarin da ya janyo hankalin duniya, inda ake kira da a tsagaita wuta, amma masu kai harin sun ƙi ji.

Mista Abdulla Shawesh ce, “aƙalla Palatinawa 1,800 ne suka jikkata, yayin da aka kashe ma’aikatan lafiya har guda 68, inda guda 100 suka jikkata, asibitoci 12 da cibiyoyin lafiya 32 suka tashi daga aiki sakamakon kai musu hari ko kuma rashin man fetur. An lalata motocin ɗaukar majinyata guda 25 sakamakon harin isra’ilawa.

Ya ƙara da cewa, “irin makaman da ake amfani da su su na zagwanye fata da ciwo, kuma sai an yi aiki na musamman ake iya yi wa ciwon magani, wanda babu irin maganin a yankin Gaza.”

Ya ce, ana yin tiyata ba tare da sinadarin allurar sa bacci ba, inda ake amfani da hasken waya kawai a kan korido (maimakon ɗakin tiyata).

Daga nan ya ƙara da cewa, yawan al’ummar da aka raba da muhallinsu a yankin Gaza sun kai kimanin miliyan 1.4 ’yan ƙasa, inda suka watsu a gurare daban-daban ba tare da cikakken samun agaji ba, domin hatta Majalisar Ɗinkin Duniya abin na neman gagarar ta.

“Fiye da gidaje 181,000 aka lalata, ciki har da 20,000, waɗanda aka tasa daga aiki kacokam,” inji shi, yana mai cewa, “a West Bank kuwa Yahudawa sun aiwatar da hukuncin kisa akan Palastinawa 91 daga ranar 7 ga Oktoba, waɗanda yawancinsu yara ne. Ana tsare da Palastinawa kimanin 6.500 a yankin tun daga farkon shekara, yayin da guda 1,215 tun ranar 7 ga Oktoba aka tsare su.”

Ya kuma tuno da yadda aka yi wa wani magidanci mai suna Omar Daraghmeh ɗan shekara 58 kisan gilla ranar 8 ga Oktoba, da ɗan shekara 25 mai suna Arafat Yasser Hamdan kisa a ranar 22 ga Oktoba, saboda tsananin azaba da aka riqa gana musu a kurkuku.