Waliyyan ango sun nemi a mayar musu da sadaki don su maida inda aka aro

Daga AISHA ASAS 

Idan ba ka mutu ba, aka ce komai kana gani. Wani sabon salo, wai Bature da feƙe. A ranar Larabar da ta gabata a Jihar Sakkwato a wata unguwa da ake kira Zoramawa aka yi taro na ji da gani da ƙudirin neman auren wata yarinya da saurayinta da suka jima su na yin soyayya. 

Taron da ya ɗauki ilahirin dangin yarinyar lokaci wajen shiri na  kwalliya da kuma kayan abincin da aka shirya don tarbon dangin ango, waɗanda suka haɗa da lafiyayyun kaji da makusantan uwar amarya suka tabbatar kowacce ɗaya daga ciki an siye ta kan farashin Naira har dubu goma, kuma an gyare masu har guda huɗu, wato dai dubu arba’in. 

A vangare ɗaya, an yi shinkafa, awara, donut, har da wainar da ɗaya daga cikin ‘yan’uwan uwar suka yi alƙawarin yi a matsayin gudunmawa, sai dai ba a samu kaiwa ga uwar amaryar ba, a cewar ta, “indai masa an yi masa har ta kwano uku, amma abin ka da gidan yawa, wainar ta ɓace a cikin jama’a kafin ta iso ga waɗanda aka yi don su,” amma dai an kawo wainar guda ɗaya ga umar amarya, wadda mai gudunmawar ta ce ita ta yi saura, kuma ta nemi da ta raba biyu, ta bata rabi, don ita ma ta kai ga bakinta na salati.

Duk wannan hidima da aka yi, an yi ne don a ba wa ‘yan ango masu zuwa neman aure da kawo sadaki.

Dangin ango kam sun iso, kuma sun nema, an kuma ba su, an yanka sadaki dubu ɗari, kuɗin lefe dubu ɗari da hamsin. 

Take suka bayar da kuɗi dubu ɗari na sadaki, inda suka yi alƙawarin aiko da na lefe daga baya. Sun kawo goro da alawa da ƙiyasin su zai kai rabin kuɗin kayan da aka haɗa masu na tarbo.

A daidai lokacin da aka kammala zaman, mutane na shirin kama gaban su, waliyyan ango na kusa, suka jinkirta miƙewa, suka nemi waliyyan amarya da su mayar masu da kuɗin da suka miƙa mintuna kaɗan baya a matsayin na sadaki, domin dai angon ya aro kuɗin ne don a miƙa gaban mutane su ga an bayar, amma a dawo da shi, a mayar a inda ya karɓo, wanda suka ce, ba za su tafi su bar kuɗin ba, saboda ba su da masaniyar inda angon zai iya samun adadin kuɗin da zai iya biyan bashin, don haka waliyyan amarya su yi haƙuri, su bada kuɗin, alabarshi daga baya idan ya samu, sai ya kawo masu.

Abin tambaya, idan har suna tunanin ba su da masaniyar inda zai iya samun kuɗin na sadakin, ta yaya zai iya biyan na lefe da suka fi na sadakin yawa? Shin ko yana ma da muhallin da zai iya ajiye matar a bayan auren?

A wata majiya ta ƙud-da-ƙud ga amaryar, ta shaidawa Manhaja cewa, uwar amaryar ce ta ce za ta ara ma shi filin da ta siya wa babban ɗanta, ya yi gini, ya saka ‘yar tata, daga baya idan ya samu, sai ya yi nasa, ya mayar da abinda aka ara ma shi.