Ina so na ga yara su samu kyakkyawar kulawa – Fatima SBN

“Babban burina na ga matsalolin mata sun ragu ko da ba su tafi gabaɗaya ba”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Hajiya Fatima Suleiman Baban Nana, na ɗaya daga cikin matasan ƴan siyasa mata a Jihar Gombe, wacce kuma take taka rawar gani wajen kare haƙƙoƙin mata da ba su tallafi don inganta rayuwarsu. Mace ce mai kishin ganin mata sun samu kulawa da gatan sa za su taimaki kansu da iyalinsu. A zantawar da ta yi da wakilin Manhaja Blueprint, Abba Abubakar Yakubu, ta bayyana masa gwagwarmayar da take yi ƙarƙashin ƙungiyarta ta OPWIN, da abin da ya zaburar da ita ta shiga siyasa.

MANHAJA: Ko za ki fara da gabatar mana da kanki?

HAJIYA FATIMA: To, Salamu alaikum. Ni dai sunana Fatima Suleiman Baban Nana, amma akasari an fi kirana da Fatima SBN. Ni ƴar kasuwa ce, kuma ƴar siyasa ce, kuma ma’aikaciya ce da ke aiki tare da ma’aikatar ilimi ta Jihar Gombe. Ni ƴa ce ga babban ɗan siyasar nan, kuma tsohon Babban Sakatare ne a gwamnatin Jihar Gombe, Alhaji Suleiman Baban Nana, wanda ya taɓa riƙe muƙamin Kwamishinan Hukumar kula da harkokin ma’aikata ta Jihar Gombe.

Ko za ki gaya mana wani abu daga cikin tarihin rayuwarki?

To, Alhamdulillahi. Ni dai ƴar asalin Jihar Gombe ce daga Ƙaramar Hukumar Gombe. Sai dai an haife ni ne a garin Yola na Jihar Adamawa, daga bisani na taso a garin Bauchi, lokacin Gombe na ƙarƙashin Jihar Bauchi. Na fara karatuna a makarantar firamare ta FOMWAN da ke Bauchi, daga baya na ƙarasa firamare a garin Gombe.

Sannan na ta fi garin Maiduguri a Jihar Borno inda na yi karatuna na Sakandire a makarantar nazarin ilimin addinin Musulunci ta Alburhan. Na kuma shiga makarantar Ma’ahad Tahfizul Ƙur’an a garin Gombe. Na sake komawa Maiduguri inda na yi karatu a Jami’ar Maiduguri, sashin nazarin koyar da ilimin lafiya, inda na yi digirina na farko. Yanzu haka kuma ina aiki da ma’aikatar ilimi ta Jihar Gombe, kamar yadda na faɗa a baya. Na yi aure tun ina makarantar sakandire, yanzu haka ina da yara uku, mace ɗaya da maza biyu.

Wanne abu ne ya fara jan ra’ayinki ki ka ga ya dace ki shiga harkokin siyasa?

To, ni dai tun tasowata na tashi cikin iyalin da suke da kishin ilimi da son cigaban al’umma. Mahaifina ɗan boko ne kuma babban ma’aikacin gwamnati a lokacin, kuma akwai ƴan’uwa da dama da suke cikin hidimar siyasa, don haka na taso da fahimtar menene gwamnati kuma me ake nufi da siyasa. Amma asalin abin da na ƙarfafa min gwiwa ni ma in shiga a yi da ni shi ne, yadda na lura mata na shan wahala. Suna fama da wahalhalun rayuwa, ana amfani da su wajen yaƙin neman zaɓe, fita kaɗa ƙuri’a da halartar tarukan ƴan siyasa, amma ƙalilan ne suke samun abin da za su ci da kansu ko iyalansu.

Alhalin sun wahala wajen taimakawa ƴan takara hawa kan manyan muqaman siyasa, sai ka ga ana cin moriyar siyasa babu su a ciki. Ba a sake tunawa da su har sai wani zaven ya taho. Wannan shi ne ya ƙarfafa min gwiwar shiga siyasa, don in tunatar da manyan ƴan siyasar da suka samu dama, su riƙa tunawa da haƙƙoƙin matan da suka zave, su kyautata musu rayuwa su da iyalansu.

Tun daga lokacin da ki ka fara harkokin siyasa zuwa yanzu, wanne canji za ki iya cewa kin kawo ga mata a Jihar Gombe?

To, tabbas shigata siyasa ta yi amfani matuƙa, domin kuwa ni da abokan tafiyata, mun kusanci ƴan siyasar nan mun tattauna da su, mun kuma ga irin ƙoƙarin da suke yi a nasu ɓangaren. Sai dai kamar yadda Hausawa ke cewa ne, in dambu ya yi yawa ba ya jin mai. Wani lokacin kuma rijiya tana bayar da ruwa ne, guga sai ta hana. Ma’ana, su ƴan siyasar suna wakilta wasu wajen kula da hidimar mata, amma sai su karkatar don hidimar gabansu. Ba tare da matan sun san me ake yi ba. Don haka shigar mu ta sa mun zama kamar tsani tsakanin su da matan, muna fahimtar da su halin da matan ke ciki, da kuma abubuwan da suke buƙata daga garesu.

Saboda mazan da ke tare da su ba sa iya cike wannan giɓi da ake buƙata, tsakanin wakilan gwamnati da ɓangaren mata. Mutum na farko da ya fara wayar min da kai kuma ya taimaka na fara fahimtar yadda tafiyar siyasa take shi ne, Dr Ya’u Gimba, wanda fitaccen ɗan siyasa da ke nuna kishi ga jama’arsa.

A lokacin kin kafa ƙungiya ne ko kin jingina da wasu ƴan siyasa ne, don cimma manufofinki?

A lokacin ban fara da kafa ƙungiya ba, na fara ne da ravar ƴan siyasa, don koyon yadda tsarin ke tafiya. Domin wani lokaci kallon abu daga nesa ba ya nuna maka haƙiƙanin yadda abin ke tafiya, sai ka shiga cikinsa. Don haka na fara da shiga cikin jam’iyya ne, inda na yi rijista da Jam’iyyar PDP. Ubangidana a lokacin shi ne tsohon Gwamnan Jihar Gombe Dr Ibrahim Hassan Ɗanƙwambo, Talban Gombe, wanda yanzu shi ne sanata mai wakiltar shiyyar Gombe ta Arewa. Sannan daga bisani na samu zama ta hannun daman uwargidan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar, Gimbiya Ruƙayya Atiku Abubakar, inda na zama mai ba ta shawarwari kan harkokin mata.

Wannan ya ƙara ba ni damar kusantar ƴan siyasa sosai, muna tattaunawa da kuma ba da shawarwari ga abubuwan da za su kawo wa mata cigaba a siyasance. Daga baya lokacin gangamin yaƙin neman zaven Atiku Abubakar a matsayin shugaban ƙasa, mun kafa ƙungiyar Atikulated Women Movement, domin zaburar da mata su fita su ba da gudunmawarsu don samun nasarar Wazirin Adamawa a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP. A dalilin wannan tafiya ta ƙungiyar mun samu ƙawancen ƙungiyoyin mata fiye da ɗari da suka yi rijista a ƙarƙashin mu, don cimma muradin tafiya tare da mata a siyasa.

Yaya ki ka ji a ranki da ba ku samu nasara ba, a zaven shugaban ƙasa, kin cigaba da harkokin siyasa ko kin koma gefe?

To, ita dama siyasa tun kafin mu fara mun sani akwai samu akwai rashi. Ba kowanne lokaci ne za ka iya samun nasara ba, amma mun yi ta addu’a kan Ubangiji Allah Ya yi mana zavi na alheri, a fafutukar da muke yi. Duk da ba ɗan takarar mu ne ya yi nasara ba, amma ba mu karaya ba, don mun san ba mu faɗi zaɓe ba, an dai yi abin da aka yi ne kawai. Har yanzu muna da ƙwarin gwiwar cewa, nasara na tare da mu, tun da ɗan takarar mu na kotu tare da lauyoyinsa muna neman haƙƙin mu ta fuskar shari’a.

Sai dai duk da harkokin siyasa sun lafa, ba za mu naɗe hannu mu zauna kawai ba, dole ne mu bi sauran ƴan siyasar da suka yi nasara a ƙarƙashin jam’iyyu daban daban, mu tuna musu alƙawuran da suka yi wa mata da sauran talakawa, musamman matasa. Kuma mu jajirce wajen ganin an yi abin da ya kamata, a gwamnatance. Shi ya sa yanzu muka kafa wata ƙungiya mai suna Organisation of Progressives Women in Nigeria, OPWIN a taƙaice, muna wayar da kan mata da ƴan siyasa, da masu riƙe da muƙaman gwamnati, muhimmancin sanin nauyin da ke kansu. Kuma ƙarƙashin wannan tsari babu batun nuna wariyar addini ko siyasa, haɗin kan mata muke buƙata, daga kowacce jam’iyya ko addini.

Ta yaya ki ke ganin wannan yunƙuri naku zai yi nasara?

To, ai dama ita rayuwa komai mataki mataki ne. Mun sani cewa ba za mu samu nasara a lokaci guda ba, amma ganin irin zubin matan da muke tare da su, waɗanda yawanci sun yi siyasa ko sun yi aiki da ƴan siyasa a cikin gwamnati, da waɗanda yanzu haka ake damawa da su a matakai daban daban, ina da ƙwarin gwiwar za mu kai gacin da muke so. Yadda hukumomin gwamnati, ƴan majalisu, da wakilan al’umma za su amince mu yi tafiya tare, don cimma manufofin Dimukraɗiyya na inganta rayuwar talakawa da marasa qarfi, musamman matasa, mata, da ƙananan yara. Kuma da izinin Allah, nasara na tare da mu.

Wanne ƙalubale ne ki ke ganin mata na fuskanta, musamman a ɓangaren siyasa da gwamnati?

Waɗannan ƙalubale duk ba ɓoyayyu ba ne. Yanzu haka zancen da muke yi a sabuwar Majalisar Dokokin Jihar Gombe da aka rantsar babu mace ko guda ɗaya, dama akwai wata guda ɗaya ne amma ta faɗi a Babban Zaven 2023 da ya gabata. Ka gani muna da wannan ƙalubalen, kuma ba a Gombe kaɗai ba, kusan dukkan jihohin ƙasar nan idan ka bincika mata ƙalilan ne a majalisar jihohinsu, haka ma kuma a matakin ƙasa.

Don haka muna buƙatar gwamnati ta yi aiki da wannan dokar da ta bai wa mata damar samun wani kaso na musamman a tsarin tafiyar da gwamnati. Muna son mu ga mata a muƙamai daban daban, da za su yi amfani da damar su wajen tallafawa rayuwar mata da yara a ko’ina suka samu dama. Domin mata su shaida nasarar da suka taimaka aka samu wajen kafuwar tsarin dimukraɗiyya.

Wanne buri ki ke so ki ga kin cimma a rayuwarki?

Babban abin da nake burina na ga na cimma a wannan gwagwarmaya da nake yi shi ne na ga matsalolin mata sun ragu ko da ba su tafi gabaɗaya ba. Ran da na buɗi ido na ga wannan abin ya kasance, ba ƙaramin farin ciki zan ji a rayuwata ba. Ina burin in ga yara sun samu kyakkyawar kulawa, a ɓangaren lafiya, ilimi da tarbiyya, da makoma tagari. Ina son in ga matasan mu sun samu abin dogaro da kansu, sun daina zaman banza, shaye-shaye da aikata laifuka, saboda rashin ayyukan yi. Yara mata sun daina yawo a titi da sunan talle. Waɗannan su ne abubuwan da suke damuna a cikin rai, kuma nake kooƙarin ganin na yi amfani da duk wata dama da na samu don kawo canji a cikin al’umma.

Shin kina da burin nan gaba ki tsaya takarar wani muƙami a siyasa?

To, Allah dai shi ne ke qaddarawa bawa komai a rayuwarsa. Amma gaskiya ni a ra’ayina ba ni da tunanin tsayawa takara a siyasa, burina dai in kai ga cimma nasarar abubuwan da na sa a gabana. Kamar yadda na yi maka bayani a baya. Ina dai da ra’ayin zama babbar ƴar kasuwa.

Wacce mace ce ko waɗanne mata ne ki ke koyi da su a rayuwarki?

Mace ta farko da nake ɗauka a matsayin madubin rayuwata, ita ce mahaifiyata, wacce ba ni da kamar ta, sai kuma ta biyu Layla Ali Othman, wannan baiwar Allah tana matuqar burgeni, duk da kasancewar ni ba ta sanni ba, amma bibiyar abubuwan da take wanda ni kuma suke ƙara min ƙwarin gwiwa sosai a rayuwata.

Wanne abin koyi ki ke so ki bar wa ƴan baya, domin su ma su yi koyi da rayuwarki?

Abin da nake so mata su yi koyi daga rayuwata shi ne jajircewa. Lallai ne mace ta jajirce, nasara ba ta tava samuwa a rayuwa sai da jajircewa. Kuma in sha Allahu duk wacce ta yi koyi da haka za ta kai ga gacin da take so, a kan kowanne al’amari na rayuwa.

Wanne abu ne ya fi sa ki farinciki, ko akasin haka a rayuwarki?

Abin da ya fi sa ni cikin farinciki ko jin daɗi a zuciyata shi ne karatun Alƙur’ani da kuma yin sallah a kan lokaci. Sannan sai lokacin da muke zaune tare da mahaifinmu yana yi mana nasiha a kan rayuwa, ni da sauran ƴan’uwana, ina matuƙar jin daɗin hakan sosai.

Abin da na fi tsana a rayuwata kuwa shi ne, a zarge ni kan abin da ban aikata ba, ko ban ma taɓa tunaninsa a zuciyata ba. Yana ɗaga min hankali sosai, har ina kasa iya barci ko cin abinci, saboda baƙinciki.

Wanne saƙo ki ke da shi ga sauran mata ƴan gwagwarmayar kare haƙƙoƙin jama’a, da waɗanda ku ke ayyuka tare?

Saƙona gare su shi ne mu cigaba da gwagwarmaya, mu tsarkake zuciyoyinmu, mu yi wa al’umma aiki tsakani da Allah. Kar mu yi tunani kan me za mu samu. Mu fi mayar da hankali ga taimakon da za mu wa jama’a, da na ƙasa da mu, da yardar Allah, ubangiji zai ba mu ladan abin da muke yi, ba a duniya kaɗai ba, har ma a lahira.

Mun gode.

Ni ma na gode sosai.