Jihohin Nijeriya biyar da aka fi kashe mutane bayan hawa mulkin Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaba Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya cika shekara ɗaya a kan karagar mulki bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023 a matsayin Shugaban Nijeriya.

Ƙasar da ta kwashe shekaru tana fama da matsalar tsaro a kusan dukkanin yankunanta shida.

Duk da cewa al’ummar yankunan da aka fi fama da matsalar tsaron sun yi fatan a samun sa’ida bayan karɓar sabuwar gwamnati, amma wasu na ganin cewa matsalar tamkar ƙara muni ta yi.

An ci gaba da fuskantar matsalar masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da yi wa mutane kisan gilla a jihohin Arewa maso Yamma, Boko Haram ta ci gaba da kai hare-haren sari-ka-noƙe da dasa nakiyoyi a Arewa maso Gabas, sannan an ci gaba da samun kashe-kashe na ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya a Kudu maso Gabas.

Ko a washegarin ranar da aka rantsar da sabuwar gwamnati, ‘yan bindiga sun kashe mutum 25 a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara, ciki har da wani jagoran ‘yan sa-kai.

Sai dai gwamnati na cewa tana bakin ƙoƙarinta.

Ta hanyar nazari kan rahotan kamfanin Beacon Consulting mai nazari kan tsaro a Nijeriya, mun duba jihohi biyar na ƙasar da aka fi hallaka mutane tun bayan rantsar da gwamnatin ta Bola Ahmed Tinubu:

 1. Jihar Borno
  Borno na cikin jihohin Nijeriya da suka fi cin karo da kalubalen tsaro a tarihin Nijeriya sanadiyyar rikicin Boko Haram wanda ya samo asali a shekarar 2009.

Duk da nasarorin da dakarun gwamnati suka samu a tsawon shekarun yaƙi da ƙungiyar, har yanzu mayaƙan Boko Haram na nuna tasirinsu nan da can.

Shi ya sa ma jihar ta Borno ta yi zarra a yawan mutanen da aka kashe tun bayan hawan Bola Tinubu a matsayin Shugaban Nijeriya.

Yawancin hare-hare da suka yi sanadiyyar kashe-kashe a jihar sun faru ne sanadiyyar ayyukan ƙungiyoyin masu iqƙirarin jihadi kamar ta Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati al Jihad da ISWAP, sai kuma wasu lokuta da dakarun Nijeriya suka yi masarar murƙushe mayaƙan na Boko Haram.

A jimilla, rahoton Beacon Consulting ya nuna cewa an kashe fararen hula 2,070 a jihar ta Borno tun daga watan Yunin shekara ta 2023 bayan hawa mulkin Shugaba Tinubu.

Wani abin kuma shi ne yadda ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadin suka riqa kai wa juna hari, lamarin da ya haifar da salwantar rayuka da dama tare da ƙara yawan adadin mutanen da aka kashe a jihar.

Misali, akwai harin da Jama’atu Ahlis Sunna lidda’awati wal jihad ta kai a ranar 19 ga watan Oktoba kan mayaƙan ISWAP a ƙaramar hukumar Abadam inda ta kashe mayaƙa 40.

Haka nan a ranar 14 ga watan Afrilun 2024 kungiyar ta Jama’atu Ahlis Sunnah ta kai wa mayaƙan ISWAP hari a ƙaramar hukumar Kukawa, inda ta kashe wasu mutunen 100.

Sai dai wasu daga cikin munanan hare-haren da ƙungiyar ta Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati al Jihad ta ƙaddamar kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba sun haɗa da wanda ta kai ranar 19 ga watan Agusta a yankin Maiduguri inda ta kashe mutum kimanin 100.

A ranar 15 ga watan Yunin na 2023 kuma mayaqan Boko Haram sun kai hari kan wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Jere, inda suka kashe mutum 15.

Sai dai duk da haka sojoji sun samu nasara sosai a kan mayaƙan Boko Haram, kamar yadda sojin sama na Nijeriya suka kashe mayaƙan ƙungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah guda 100 a ƙaramar hukumar Gwoza a ranar 11 ga watan Yunin shekarar 2023.

Ƙananan hukumomin da aka fi kashe mutane tsakanin wannan lokaci a jihar ta Borno su ne Marte inda aka kashe mutum 402, sai kuma Kukawa inda aka kashe mutum 347.

 1. Jihar Zamfara
  Ba abin mamaki ba ne yadda jihar Zamfara ta zamo ta biyu cikin jihohin da aka fi kashe fafaren hula Nijeriya tun bayan kama mulkin Shugaba Tinubu.

Hakan kuwa ba zai rasa nasaba da yadda jihar ta yi qaurin suna wajen fama da hare-haren ‘yan bindiga masu satar mutane domin karɓar kuɗin fansa ba.

Za a iya cewa Zamfara ce jihar da ta fi kowace fama da wannan matsala tun bayan hawan Tinubu kan mulki.

‘Yan bindiga sun ci gaba da cin karensu babu babbaka, suna kisa a ƙauyuka da kan manyan hanyoyi, da kwashe mutane suna korawa daji tare da tarwatsa al’ummu daga matsugunansu.

Lamarin ya ci tura duk da cewa gwamnan jihar Dauda Lawal ya ƙaddamar da ƙungiyar ‘yan sa-kai ta Askarawan Zamfara, ga shi kuma karamin ministan tsaro na Nijeriya, Bello Matawalle ya fito ne daga jihar.

Alƙaluman kamfanin Beacon Consulting sun nuna cewa an rasa ran fararen hula 761 daga 30 ga watan Yunin 2023 zuwa Mayun 2024.

Tun a cikin watan da aka rantsar da shugaban ƙasar ne aka ci gaba da kashe mutane, inda ‘yan bindiga suka halaka mutum 25 a Maru, sannan wasu ‘yan bindigan suka ƙara kashe mutum 25 a Maradun tare da sace yara mata sama da 30.

A ranar 20 ga watan Yulin 2023 kuma wasu mahara sun kashe sojoji 7 da wasu fararen hula 28 duk a qaramar hukumar ta Maru.

A ranar 11 ga watan Mayun 2024 an kashe mutum 49 a qaramar hukumar Anka, lokacin da ‘yan bindiga suka kai farmaki a ƙauyukan Yar Sabaya da Farar ƙasa da Duhuwa.

Sannan a baya-bayan nan ranar 11 ga wannan wata na Mayu 2024 rikici tsakanin ƙungiyoyin ‘yan bindiga a ƙaramar hukumar Anka ya yi sanadin kashe mutum 23.

Ƙananan hukumomi biyu da aka fi kashe mutane a jihar su ne Maru inda aka kashe mutum 329, sai Tsafe inda aka kashe mutum 112.

 1. Jihar Filato
  Filato jiha ce da ta yi ƙaurin suna a tashe-tashen hankula masu nasaba da rikici tsakanin manoma da makiyaya da kuma tsakanin ƙabilu.

An samu ƙaruwar irin waɗannan rikice-rikice gabanin babban zaɓen Nijeriya na 2023 sannan hakan ya ci gaba da tasiri har bayan rantsar da sabuwar gwamnati.

Daga ranar da aka rantsar da Bola Tinubu zuwa watan Maris na 2024 an kashe fararen hula 560, kamar yadda alƙaluman kamfanin Beacon Consulting suka nuna.

Hari na farko mafi muni a jihar ta Filato bayan kama mulkin Tinubu shi ne wanda aka kai a ƙaramar hukumar Riyon, inda aka kashe mutum 21.

Haka nan ranar 18 ga watan Yuni an kashe mutum 22 a ƙaramar hukumar Mangu, aka kuma ƙara kashe mutum 15 a ƙaramar hukumar ta Mangu ranar 20 ga watan na Yuni sanadiyyar faɗa tsakanin wasu al’ummu.

Ƙananan hukumomin da aka fi rasa rai a cikinsu a jihar ta Filato cikin wannan lokaci su ne Bokkos inda aka kashe mutum 174, sai mai biye mata ƙaramar hukumar Mangu inda aka kashe mutum 149.

 1. Jihar Benuwe
  Ta huɗu a cikin jerin ita ce jihar Benue da ke yankin arewa maso tsakiyar Nijeriya inda aka kashe mutum 542.

Rikice-rikice a jihar Benue na kamanceceniya da na jihar Filato, inda ake samun taƙaddama tsakanin manoma da makiyaya ko kuma tsakanin ƙabilu masu hamayya da juna.

Tun kafin Tinubun ya cika mako guda aka ci gaba da kashe-kashe a jihar ta Benue, inda a ranar uku ga watan Yunin 2023 aka kashe mutum 25 a ƙaramar hukumar Katsina-Ala lokacin da wasu mahara suka far wa al’umma.

Haka nan a ranar 8 ga watan Yuli wasu maharan sun kashe mutum 24 a ƙaramar hukumar Ukum.

A baya-bayan nan kuwa wasu maharan sun kashe mutum 10 a ƙaramar hukumar Agatu, ranar 25 ga wannan wata na Mayun 2024.

Ƙananan hukumomin da aka fi asarar rai a jihar Benue a tsakanin wannan lokaci su ne Ukum inda aka kashe mutum 136, sai Agatu mai mutum 58 da kuma Gwer West ita ma mai mutum 58.

 1. Jihar Kaduna
  Kaduna ita ce jiha ta biyar da aka fi kashe mutane a Nijeriya tun bayan kama mulkin Bola Ahmed Tinubu.

Kamar takwararta ta arewa maso yamma – jihar Zamfara, babbar matsalar da ta fi addabar Kaduna ita ce ta ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, sai kuma wasu lokutan da akan samu rikici tsakanin ƙabilu ko kuma manoma da makiyaya a kudancin jihar.

Matsalar garkuwa da mutanen ta hana al’umma sakat a wasu yankunan ƙananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa da Kajuru.

Alƙaluman kamfanin Beacon Consulting sun nuna cewa ana kashe mutum 400 tsakanin watan Yunin 2023 zuwa Mayun 2024.

A ranar ɗaya ga watan Janairu wasu ‘yan bindiga suka kai hari a ƙaramar hukumar Birnin Gwari inda suka kashe ‘yan sintiri 19, sannan duk a ranar wasu ‘yan sa-kai ɗin suka kashe ‘yan bindiga 40 a ƙaramar hukumar.

A ranar 18 ga watan Fabrairu kuwa wasu ‘yan bindiga suka dirar wa wani ƙauye a qaramar hukumar Kajuru, inda suka kashe mutum 12 da ƙona gidaje kimanin 17.

Sannan wani abu da ya ɗauki hankalin duniya shi ne yadda wasu ‘yan bindiga suka shiga ƙauyen Kuriga na ƙaramar hukumar Chikun a ranar 7 ga watan Mayun 2024 inda suka sace yara ɗalibai da dama, an ceto su daga baya, sai dai malami ɗaya ya rasa ransa.

A baya-bayan nan wasu mahara sun kashe mutum shida a ƙaramar hukumar Kajuru a ranar 19 ga wannan wata na Mayu.

Birnin Gwari ce ƙaramar hukumar da aka fi kashe mutane a cikinta a cikin shekara ɗaya ta mulkin Tinubu, inda aka kashe mutum 105.

Ƙaramar hukumar da ke biye mata a wannan harka ita ce Kauru mai mutum 46.

Duk da cewa gwamnatin Tinubu ta gaji matsalar tsaro ne daga gwamnatocin baya amma gazawar ta wajen yayyafa wa al’amarin ruwa abu ne da zai iya karya gwiwar al’umma.

Tabbas, ba abu ne mai yiwuwa ba a ce Tinubun ya kawar da ilahirin matsalar tsaron da ya gada cikin shekara ɗaya ba, amma rashin ganin sauƙi a matsalar zai iya zama tamkar Larabar ba ta nuna cewa Juma’ar za ta yi kyau ba.

Saboda haka akwai buƙatar gawamnatin ta Shugaba Tinubu ta fito da tsare-tsaren da za su taimaka wajen warware wannan mugun ƙulli.