Daga BASHIR ISAH
Aƙalla mutum 20, ciki har da jami’an kwana-kwana da ‘yan banga suka jikkata sakamakon gobarar tankar mai da ta auku ranar Juma’a a Jihar Kaduna.
MANHAJA ta kalato cewar, gobarar ta auku ne a daidai lokacin da ake sauke mai daga tankar a wani gidan mai da ke Rigasa cikin yankin Ƙaramar Hukumar Igabi a jihar.
Da yake tabbatar da aukuwar iftila’in, Daraktan Hukumar Kwana-kwana na Jihar, Paul Aboi, ya ce gobarar ta ji wa wasu jami’ansu su biyar da wasu ‘yan bangan jihar haɗi da wasu masu wucewa da dama raunuka.
Jami’in ya ɗora alhakin faruwar gobarar a kan gidan man saboda sakacinsa, yana mai cewa ba daidai ba ne sauke fetur da rana tsaka.
Daga nan, Aboi ya gargaɗi gidajen mai da su guji jefa rayuwar jama’a cikin hatsari ta hayar sauke fetur a irin lokacin da ya dace.
