Kasashen Waje

Yaƙin Iran: Da yiwar Turkiyya ko Pakistan ta karɓi baƙuncin tattaunawar tsagaita wuta

Yaƙin Iran: Da yiwar Turkiyya ko Pakistan ta karɓi baƙuncin tattaunawar tsagaita wuta

Wani babban jami’in Iran ya bayyana cewa ƙasar Pakistan ta isar da wata muhimmiyar shawara daga Amurka zuwa Iran, inda ake duba yiwuwar gudanar da tattaunawa a ƙasar Pakistan ko kuma Turkiyya domin rage zafin rikicin da ke ci gaba da addabar yankin Tekun Gulf. Jami’in, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida cewa wannan mataki na daga cikin alamun farko da ke nuna yiwuwar Iran ta fara la’akari da hanyoyin diflomasiyya, duk da cewa a fili gwamnatin Tehran tana ci gaba da musanta cewa akwai wata tattaunawa da ke gudana da Amurka. Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta…
Read More
Ƙungiyar Iran ta kutsa imel ɗin Daraktan FBI

Ƙungiyar Iran ta kutsa imel ɗin Daraktan FBI

Daga USMAN KAROFI Wata ƙungiyar masu satar bayanai da ake danganta da Iran ta samu damar shiga asusun imel na Daraktan FBI, Kash Patel, sannan ta wallafa hotuna na sirri da wasu bayanai a yanar gizo, rahoton kafofin watsa labarai na Amurka ya bayyana ranar Juma’a. Ƙungiyar Handala Hack Team ta ce Patel “za ya ga sunansa a cikin jerin waɗanda aka samu nasarar satar bayanansu”. Rahoton CNN ya bayyana cewa imel ɗin da aka sace sun haɗa da na sirri, harkokin kasuwanci da na tafiye-tafiye, wanda suka shafi shekaru 2011 zuwa 2022, kafin Patel a nada shi Daraktan FBI…
Read More
Yaƙin Iran: Trump na zargin kafafen labarai da ƙoƙarin raunana nasararsa a yaƙin

Yaƙin Iran: Trump na zargin kafafen labarai da ƙoƙarin raunana nasararsa a yaƙin

A yayin da yaƙin Iran ke ci gaba da jefa Gabas ta Tsakiya cikin rikici, wata sabuwar guguwa ta taso a cikin Amurka, inda Shugaba Donald Trump da manyan na hannun damansa suka tsananta kai hari kan kafafen yaɗa labarai da suke ba da rahoto kan yaƙin. Sabon salo da kalaman da ke fitowa daga Fadar White House sun nuna cewa gwamnatin Trump na kallon yadda ake yaɗa labaran yaƙin a matsayin wani muhimmin fage na gwagwarmaya, musamman a daidai lokacin da goyon bayan jama’a ga yaƙin ke fuskantar rauni. Tun shekaru da dama, Donald Trump ya yi suna wajen…
Read More
Gobarar Kerzers Switzerland: Mutane shida suka rasa rayukansu bayan wani ya kunna wuta a jikinsa

Gobarar Kerzers Switzerland: Mutane shida suka rasa rayukansu bayan wani ya kunna wuta a jikinsa

Aƙalla mutane shida sun rasa rayukansu yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon wata gobara mai muni da ta tashi a cikin wata bas a garin Kerzers da ke yammacin ƙasar Switzerland. Hukumomin ‘yan sanda sun bayyana cewa gobarar ta faru ne a daren Talata, kuma akwai alamun cewa wani mutum a cikin bas ɗin ne ya janyo gobarar da gangan. Kakakin ‘yan sandan yankin Fribourg, Frederic Papaux, ya ce binciken farko ya nuna cewa wani mutum da ke cikin bas ɗin na iya aikata wannan aiki da gangan. Rahotanni daga wasu kafafen watsa labarai sun nuna cewa mutumin ya…
Read More
Mu ne za mu yanke hukuncin lokacin da yaƙin zai ƙare – Martanin Iran kan kalaman Trump na yaƙinsu ya kusa ƙarewa

Mu ne za mu yanke hukuncin lokacin da yaƙin zai ƙare – Martanin Iran kan kalaman Trump na yaƙinsu ya kusa ƙarewa

Rundunar juyin juya halin ƙasar Iran ta yi watsi da kalaman Shugaba Donald Trump na cewa yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar akan Iran ya kusa ƙarewa, yayin mayar da martani akan furucin shugaban Amurkan. Trump ya bayyana a wani taro a Florida cewa Amurka ta samu gagarumar nasara a yaƙin, kuma akwai yiwuwar kawo ƙarshensa nan kusa. Shugaban Amurka ya ce Iran na shirin kai hari kan Amurka kuma tana ƙoƙarin farfado da shirinta na Nukiliya. A kan yiwuwar kai hari kan sabon jagoran addinin Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei, Trump ya ce ba abu ne da ya kamata…
Read More
Majalisar Birtaniya ta rusa tsarin kujerun gado na sarakuna a majalisar dattijai 

Majalisar Birtaniya ta rusa tsarin kujerun gado na sarakuna a majalisar dattijai 

Majalisar dokokin ƙasar Birtaniya ta amince da wata sabuwar doka da za ta kawo ƙarshen tsohon tsarin da ke bai wa wasu ‘yan aristocrats damar zama mambobin Majalisar Dattijai saboda gadon sarauta kawai. Sabuwar dokar, wadda aka fi sani da Hereditary Peers Bill, ta samu amincewa a daren Talata a Majalisar Dattijai ta ƙasar, lamarin da ya kawo ƙarshen wani tsarin siyasa da ya shafe ƙarni da dama yana aiki a Birtaniya. Wannan mataki wani muhimmin ɓangare ne na shirin gyaran majalisar da gwamnatin Firaminista Keir Starmer ta jam’iyyar Labour ta ɗauka domin sabunta tsarin majalisar dokokin ƙasar. A cikin…
Read More
Za su farmake mu cikin mako guda, inji Trump bayan gano ƙarfin makaman Iran ya wuce yadda yake tunani

Za su farmake mu cikin mako guda, inji Trump bayan gano ƙarfin makaman Iran ya wuce yadda yake tunani

Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce Iran tana da makamai masu linzami sama da yadda ake tunani da fari, wanda hakan ya sa take shirin kai wa Amurka hari. Trump ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin jawabi ga ‘yan majalisa na jam’iyyarsa ta Republican a taron shekara-shekara na nazarin tsare-tsaren da aka yi a Florida. A cewarsa, ƙasar za ta iya kai musu hari cikin mako ɗaya duba da shirin da suka yi wa yaƙin. Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan jawabin Shugaban na Amurka cewa hare-haren soji da take kai wa Iran ka iya ƙarewa nan…
Read More
Iran da ƙasashen Musulunci: Abinda ya taɓa gira fa shi ne zai taɓa ido

Iran da ƙasashen Musulunci: Abinda ya taɓa gira fa shi ne zai taɓa ido

Daga AISHA ASAS A can kwanakin bayan a shafin Iyali mun taɓa darasi kan yadda rarabuwar kawuna a addini ya jefa Musulunci cikin halin da yake a yanzu. Inda a halin da muke ciki kowane ɓangare na kallon ɗaya a matsayin wanda ba muslmi ba. Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da ya rage ƙarfin Musulunci duk da tarin mabiya da yake da shi. Shafin ƙasashen Waje na wannan makon zai tattauna kan yaƙin Iran da yadda ƙasashen Musulunci suka koma gefe suna kallo yayin da wasu ke ganin hakan a matsayin daidai. Tun bayan juyin juya halin Musulunci na…
Read More
Ana yi wa ɗan jagoran addinin Iran tayin zama shugaba yayin da Isra’ila ke fafutukar halaka shi

Ana yi wa ɗan jagoran addinin Iran tayin zama shugaba yayin da Isra’ila ke fafutukar halaka shi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mojtaba Khamenei, ɗan marigayi shugaban addinin Musulunci na Iran Ali Khamenei, yana cikin manyan masu fafutukar maye gurbin mahaifinsa a matsayin sabon shugaban ƙasar. Ana sa ran za a naɗa magajin Khamenei ta hannun babban kwamitin malamai, Majalisar Masana, inda ɗaya daga cikin membobinta, Ahmad Khatami, ya shaida wa kafofin watsa labaran gwamnatin Iran a ranar Laraba cewa suna fatan kaɗa ƙuri'a "da wuri-wuri". Masu fafatawa a babban matsayi sun haɗa da Alireza Arafi, ɗaya daga cikin mambobi uku na majalisar riƙon ƙwarya da ke tafiyar da ƙasar, mai tsaurin ra'ayi Mohsen Araki, har…
Read More
Trump ya gabatar da jawabi mafi tsawo a tarihi yayin da Amurkawa ke ƙara ƙorafi kan tattalin arziki

Trump ya gabatar da jawabi mafi tsawo a tarihi yayin da Amurkawa ke ƙara ƙorafi kan tattalin arziki

Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana a jawabin sa na shekara-shekara ga Majalisar Dokoki cewa ya kawo “zamanin zinariya na Amurka,” yana ƙoƙarin nuna nasarori duk da ƙarancin amincewa daga ‘yan ƙasa da kuma ƙarin tashin hankali a zuciyar masu jefa ƙuri’a kafin zaɓen tsakiyar wa’adi a watan Nuwamba. A farkon sa’o’i na jawabin da aka watsa ta talabijin, Trump ya mai da hankali kan tattalin arziki, inda ya ce ya rage hauhawar farashin kaya, ya sa kasuwar hannayen jari ta kai matsayi mafi girma a tarihi, ya sanya dokokin rage haraji, sannan ya sauƙaƙa farashin magunguna. Sai dai…
Read More